Author: Wafsym

Fasinjoji da dama sun jikkata bayan wani jirgin ƙasa da ke jigila tsakanin Abuja zuwa Kaduna ya sauka daga layin dogo sakamakon cin karo da wani abu a kan hanyarsa. Lamarin ya faru ne yau Litinin a kusa da Asham a kan layin dogon da ke tsakanin Abuja da Kaduna, lamarin da ya jefa fasinjojin cikin fargaba. Shugaban Hukumar Sufurin Jiragen Ƙasa (NRC), Kayode Opeifa, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an tura tawagar agajin gaggawa nan take bayan samun rahoton hatsarin. Binciken farko ya nuna cewa jirgin ya kauce daga hanyarsa ne bayan ya yi karo da…

Read More

Tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, ya bayyana dalilin da ya sa bai ɗaga hankalinsa ba bayan rasa manyan muƙamai biyu a rayuwarsa. Sanusi II, ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a taron lakcar azumi ta shekara-shekara ta Fola Adeola (Fola Adeola Annual Ramadan Lecture). Mun Ceto Nijeriya Yayin Da Take Gab Da Dilmiyewa – Shugaba Tinubu A wajen taron, ya yi magana kan muhimmancin haƙuri da kuma yadda dogaro da Allah Ya taimaka masa wajen shawo kan ƙalubalen da ya fuskanta. Ya ce mutane da dama suna kuskuren danganta…

Read More

Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin duba harajin da aka ɗora wa gidan jaridu da Rediyo da talabijin domin ƙarfafa masana’antar watsa labarai da kuma inganta rawar da take takawa a kundin tsarin mulki. Shugaban ya yi wannan alkawari ne a ranar Juma’a a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, yayin wani taron buda baki da ya yi tare da shugabannin kafafen yaɗa labarai. Tinubu ya yaba wa masu gidajen jarida, editoci da ‘yan jarida bisa rawar da suke takawa wajen sanar da al’umma bayanai, halin da kasa ke ciki, samar da guraben aiki da kuma tabbatar da…

Read More

Har yanzu babu ƙasa ko guda 1 da ta amsa buƙatar Donald Trump wajen aika jirgi mashigin Hormuz cikin ƙasashe 5 da shugaban na Amurka ya nemi su aike da jiragen yaƙinsu na ruwa tare da sojojinsu don yiwa jiragen dakon mai rakiya a mashigin na Hormuz da Iran ta kulle. A jiya Asabar ne Trump ya nemi ƙasashen China da Faransa da Japan da Korea ta kudu da kuma Birtaniya kan su aike da jiragen yaƙi zuwa mashigin na Hormuz don ƙalubalantar shingen da Iran ta sanya wanda ya hana safarar makamashi. Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin samar…

Read More

Gwamnatin tarayya tare da guiwa da Gavi da ke samar da magunguna da asusun kula da ƙananan yara (UNICEF), za ta sanya wutar sola a asibitocin a matakin farko (PHCs) guda 371 a jihohi 16 ciki har da babban birnin tarayya Abuja domin inganta allurar rigakafi da kula da marasa lafiya musamman a yankunan da aka bi buƙatar tallafin. An ƙaddamar da fara shirin saka wutar ne a wani biki da hukumar bunƙasa asibitoci a matakin farko (NPHCDA) ta shirya a Abuja a ranar Alhamis. Kano, Sokoto da jihohi tara na iya fuskantar ɓarkewar cutar sankarƙau – NiMet A yayin…

Read More

Hukumar kula da yanayi ta NiMet ta fitar da gargaɗi cewa jihohi 11 na Arewa, ciki har da Kano da Sokoto, na cikin haɗarin fuskantar barkewar cutar sankarƙau yayin da yanayin bushewar kakar rani ke ƙaruwa. Sanarwar ta ce cutar sankarƙau tana shafar abubuwan da ke bayar da kariya ga kwakwalwa da kashin baya, kuma mafi yawan lokuta tana faruwa ne sakamakon kwayar cutar Neisseria meningitidis. Ayyuka Takwas Masu Tarin Lada A Kwanaki 10 Na Ƙarshen Watan Ramadan Hukumar ta bayyana cewa cutar na yaduwa ta hanyar numfashi, musamman a wuraren cunkoson mutane ko inda iska ba ta isa sosai.p…

Read More

A yayin da aka shiga kwana goman ƙarshe a watan Ramadan, ga tunarwar wasu muhimman ayyukan lada da ya kamata a dage da su a cikin watan mai alfarma. Fitaccen malamin Musulunci, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya bayyana cewa riƙo da su yana da muhimmanci saboda tarin lada da aka tanadar wa mai aikata su: Kotu ta haramta wa Aiyedatiwa neman wani wa’adin gwamna a Ondo Itikafi: Ana so mutum idan mutum yana da hali ana ya shiga Itikafi, inda da lazimci bautar Allah. Mutum, namiji ko mace, na iya Itikafi na tsawon kwanakin ko na iya abin da ya…

Read More

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Akure, Babban Birnin Jihar Ondo, ta yanke hukuncin cewa Gwamna Lucky Aiyedatiwa bai da damar sake tsayawa takarar wani wa’adin mulki a kujerar. Da yake gabatar da hukuncin a ranar Alhamis, Mai Shari’a Toyin Bolaji Adegoke ya bayyana cewa kundin tsarin dokokin Nijeriya na 1999 (da aka yi wa kwaskwarima) bai ba wa zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, mataimakin shugaban ƙasa, gwamna ko mataimakin gwamna damar cigaba da riƙe muƙamin ba na tsawon sama da shekaru takwas. Jirgin sojin Amurka ya yi hatsari a Iraƙi Kotun ta yi wannan hukunci ne bayan gabatar da…

Read More

Wani jirgin sojin Amurka ya yi hatsari a Iraƙi, kamar yadda rundunar sojin Amurka ta tabbatar. Jirgin sojin na KC-135 ya faɗo ne bayan wani “hatsarin” da ya shafi wasu jirage biyu. Rundunar sojin Amurka ta ce “ana ci gaba da aikin ceto” a yammacin Iraƙi – abin da sojoji suka ce ya faru ne a “yankin da ba na maƙiya ba.” “Lamarin ba ya faru ba ne a yankin da ake yaƙi ko kuma musayar wuta,” in ji sanarwar. Jirgi na biyu da lamarin ya shafa ya sauka lafiya, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Babu dai tabbas kan adadin…

Read More

Fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ta sanar da rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano, cewa ta fara shirye-shiryen gudanar da bukukuwan Hawan Salla idan an kammala azumin watan Ramadan. Wannan na cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 7 ga watan Maris, 2026, wadda aka aike wa Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori. Jami’an NDLEA Sun Kama Mutane 56 A Wuraren Hada-hadar Miyagun Ƙwayoyi A Kano Fadar ta ce za a gudanar da bukukuwan hawan sallar daga fadar sarkin da ke unguwar Nassarawa a Kano.

Read More