Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta kama wasu matasa 21 a wani otel da ke yankin Kureken Sani a ƙaramar hukumar Kumbotso bisa zargin aikata abubuwan da suka saɓa wa dokokin addini. Mataimakin Babban Kwamandan hukumar, Dakta Mujahid Aminuddeen, ya tabbatar wa jaridar Daily Trust faruwar lamarin, inda ya ce an kama mata 11, wasu daga cikinsu na da shekaru tsakanin 17 zuwa 25. Kotu ta ba da umarnin kama shugaban PDP Tanimu Turaki Ya ƙara da cewa an kama maza 10, mafi yawansu matasa da shekarunsu ba su wuce 30 ba. A cewarsa, an cafke mutanen ne…
Author: Wafsym
Babbar Kotu a birnin tarayyar Najeriya Abuja, ta ba da umarnin kama shugaban tsagin jam’iyar PDP Tanimu Turaki. Jaridun ƙasar sun ruwaito cewa mai shari’a Peter Kekemeke, ya ba da umarnin ne bayan da Turaki ya ƙi bayyana a gaban kotun, domin bayar da bahasi kan wani zargi da Babban Sufetan ƴansandan ƙasar ya shigar a kan sa. A cikin ƙarar, rundunar ƴansandan ƙasar ta yi zargin cewa shugaban tsagin PDPn ya gabatar da bayanan ƙarya a wani ƙorafi da ya shigar a shekarar 2022. Mai shari’a Kekemeke, ya ce babu wata hujja da Turaki ya bayar na ƙin bayyana…
Gwamnatin jihar Sokoto, ta yi kira ga matan jihar su zama masu kula da mai da hankali yayin girki da tukwanen gas. Gwamnan jihar Ahmad Aliyu ne ya bayyana haka lokacin zuyarar jaje bayan wata gobara ta tashi a yankin Igwai har ta yi sanadin mutuwar ɗaya daga cikin hadimansa. Bayanai sun ce gobarar ta tashi ne sanadin girki da gas, lamarin da ya kai ga rasa ran da kuma asarar dukiya. kula sosai a lokacin da suke amfani da gas domin girki a cikin gidajensu. A lokuta da dama dai gas ɗin girki kan haddasa gobara a wasu sassan…
Hukumar Zabe ta jihar Kano KANSIEC ta rantsar da Honarabul. Ali Musa Ɗanmaliki, (Hardwoker) a matsayin halartaccen shugaban karamar hukumar Kumbotso a Kano. Hukumar ta rantsar da Hardwoker, ne a yau Talata, bayan sauke Abdullahi Ghali Basaf daga shugaban karamar hukumar Kumbotso, yayin da aka maye gurbin sa da Ali Musa. Matatar Ɗangote ta fitar da tan 456,000 na man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika Bayan hukuncin babbar kotun jihar Kano na sauke Ghali Abdullahi Basaf daga shugabancin ƙaramar hukumar Kumbotso, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano ta mika shedar lashe zaɓe ga Hon. Ali Musa Hardworker. Shugaban…
Mamatar mai ta Ɗangote ta sanar da fara fitar da tataccen man fetur zuwa wasu ƙasashen Afrika, matakin da ke zuwa bayan da tayi iƙirarin wadata kasuwar cikin gida a Najeriya, duk da tsadar da yake yi a gidajen mai. Bayanai sun ce an fitar da manyan jiragen dakon man fetur guda 12 ɗauke da tan dubu 450 zuwa wasu ƙasashen Afrika biyar waɗanda rikicin gabas ta tsakiya ya fi yiwa fannin makamashinsu illa. Jami’an Hisbah Sun Kama Matasa Kusan 300 Da Suka Yi Askin Banza Da Kuma Kitso A Kano Kafafen yaɗa labarai na cikin gida a Najeriya sun…
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama matasa sama da 250 kan yin askin banza ko kuma kitse gashinsu. Mataimakin babban kwamandan hukumar, Mujahid Aminudden ne ya bayyana haka a bayanin da ya fitar game da ayyukan rundunar a bikin karamar Sallah. Ya ce daga cikin matasan akwai matuka Adaidaita Sahu da ke daukan mata a gefen baburansu. Gabanin bikin Sallar dai, hukumar ta fitar da sanarwar gargadi musamman ga matasa, kan kiyaye ayyukan da suka saba da tanadin addini da al’adun mutanen Kano.
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin ƙaramar Sallah, tare da kira gare su da su ƙara ƙaimi wajen nuna kishin ƙasa da kuma ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’umma. A wata sanarwa da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis, shugaban ya jaddada muhimmancin ci gaba da riƙe darussan da aka koya a watan Ramadan. Ya ce darussa irin su tsoron Allah, haƙuri, tausayi da sadaukarwa na da muhimmanci wajen gina al’umma mai zaman lafiya, yana mai kira ga Musulmi da su ci gaba da amfani…
Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF ta kwace kofin zakarun nahiyar Afirka na 2025 daga ƙasar Senegal, tare da bai wa Morocco nasarar zama zakarun gasar. Sanarwar da CAF ta fitar ta ce kwamitin sauraron ƙorafi na hukumar ya yanke hukuncin cewa tawagar Senegal ta karya dokokin gasar, bayan da wasu daga cikin ’yan wasanta suka fice daga filin wasa a yayin wasan ƙarshe domin nuna rashin amincewa da hukuncin alƙali. Gamayyar Ƙungiyoyin APC sun amince da kungiyar Sen Yari The Renewed Hope Network TRN Hukumar ta ƙara da cewa an ayyana Senegal da laifin watsi da wasa, wanda ya…
Kungiyoyin goyon bayan jam’iyyar APC guda dubu ɗaya da ɗari biyar (1,500) da aka yi wa rajista sun amince da marawa shirin Renewed Hope Network (TRN) na Sanata Abdul’aziz Yari a matsayin wata kafa ta musamman da aka ƙirƙira domin wayar da kan jama’a domin tabbatar da sake zaɓen Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu karo na biyu a shekarar 2027. Wata sanarwa da Mataimakin Darakta Janar na gamayyar kungiyoyin, Dakta AK Peters, ya sanya wa hannu a Abuja, ta bayyana cewa bayan wani muhimmin taro, TRN ƙarƙashin jagorancin gogaggen mai wayar da kan jama’a na APC kuma tsohon Babban Mataimaki…
Hukumar kididdiga ta Najeriya NBS ta sanar da cewa an samu raguwar farashin kayan abinci da sama da kashi 15 cikin 100 a watan Fabrairun 2026, bayan dogon lokaci na hauhawar farashi a ƙasar. A cikin rahoton Consumer Price Index (CPI) da hukumar ta fitar a ranar Litinin, an nuna cewa hauhawar farashi a Najeriya ya ragu kaɗan zuwa kashi 15.06 cikin 100 a watan Fabrairu, idan aka kwatanta da kashi 15.1 cikin 100 da aka samu a watan Janairu. Hatsarin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ya jikkata mutane da dama Rahoton ya ce wannan sauƙi na nuni da…
