Gwamnan Jihar Gombe, Muhammad Inuwa Yahaya, ya sanar da rushe Majalisar Zartarwa ta jihar, a wani mataki da ke nuna sauyi a harkokin siyasar jihar. Gwamnan, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, yayin taron Majalisar Zartarwa karo na 53 da aka gudanar a fadar gwamnati. Ko da yake bai fayyace dalilan ɗaukar wannan mataki ba, alamu na nuna cewa rushewar na da nasaba da yadda wasu daga cikin kwamishinoni ke nuna sha’awar tsayawa takara a zaɓe mai zuwa Rahotanni sun ce matakin na da nufin bai wa irin waɗannan mambobi damar bin muradunsu na siyasa ba tare da tangarɗa…
Author: Wafsym
Shugaban hukumar zaɓen Najeriya Farfesa Joash Amupitan ya gargaɗin gidajen yaɗa labarai kan yaɗa labaran bogi, yana gargaɗin cewa sahihancin zaɓen 2027 na wuyan yadda kafafen yaɗa labaran Najeriya suke bayyana abubuwan da ke faruwa. Shugaban ya bayyana haka ne a yayin taron kafafen yaɗa labarai Najeriya karo na 81 da ya gudana a yau Laraba, inda ya nanata cewa fagen yaɗa labarai ya zama wani sabon dandalin yaƙin neman zabe na zamani. Gwamnatin Kano ta musanta hannu a yarjejeniyar fili a makarantar FGC Yana cewa babu wata barazana kan gudanar da sahihin saɓe, sai dai yadda kafafen yaɗa labarai…
Gwamnatin Jihar Kano ta musanta zargin cewa tana da hannu a wata yarjejeniyar musayar fili da ake dangantawa da Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kano (FGC Kano). Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na Gwamnan jihar, Mustapha Muhammad, ya fitar a ranar Litinin. A cikin sanarwar, gwamnatin ta bayyana karara cewa ba ta da hannu a kowace irin yarjejeniya, tattaunawa ko wata alaka da aka yi dangane da wannan fili. Ta kuma jaddada cewa Kwalejin Gwamnatin Tarayya ta Kano tana karkashin ikon Gwamnatin Tarayya ne ta hannun Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya, wadda ita kadai ke…
Ya mai girma Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Ahmad Sekure a matsayina na dan karamar hukumar Tarauni na rubuta wannan wasika ne saboda kira a gareka, a matsayin ka na shugaban al’umma wanda suka amince maka zama shugaban su domin suna da kyakkyawan yakinin cewa zaka musu adalci, kare rayuwar su, tallafa musu da ilimi da ayyukan yi. Ina mai kira da jan hankali dangane da batun sauya fasalin daya daga cikin kasuwannin da suke karkashin kulawar karamar hukumar Tarauni wato kasuwar ‘Yar Kasuwa dake unguwar Gyadi-Gyadi kuma mazabar Gyadi-Gyadi Kudu wacce take mallakin daidaikun mutane ciki harda marayu da…
Kungiyar tsoffin daliban makarantar FGC ta Kano, mai suna FGCKOSA ta aike da ƙorafi ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu bisa abinda ta kira da wawashe katafaren filin makarantar. Daily Nigerian Hausa ta gano cewa ma’aikatar ilimi ta ƙasa da haɗin gwiwar wani kamfani, Pluck Global Company Ltd. sun kulla yarjejeniyar yanka wa da yin gine-gine a filin, wanda a ke sa ran gobe Litinin za a ƙaddamar da aikin a harabar makarantar . Shugaba Tinubu ya amince da biyan bashin ₦3.3tn don inganta wutar lantarki Takardar korafin ta samu saka hannu na haɗin gwiwa da shugaban ƙungiyar na duniya,…
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da shirin biyan bashin naira tiriliyan 3.3 domin warware tsofaffin basussukan da suka daɗe suna addabar ɓangaren wutar lantarki a Najeriya. Sanarwar fadar shugaban ƙasa ta ce bashin ya taru ne daga shekarar 2015 zuwa 2025, kuma an cimma yarjejeniya kan adadin domin kawo ƙarshen matsalar cikin gaskiya. Barazanar Wike ta harbin ɗan jarida ta jawo alla-wadai daga ƙungiyoyi A sanarwar da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar ya ce, an riga an fara aiwatar da shirin, inda kamfanonin samar da wuta 15 suka rattaba hannu kan yarjejeniyar biyan…
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya fuskanci suka daga jama’a bayan ya ce da zai samu dama da ya “harbi” mai gabatar da shirin talabijin, Seun Okinbaloye na Channels TV. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa Wike ya yi furucin ne yayin da ya ke mayar da martani kan wani wani tsokaci da ɗan jaridar ya yi a shirin Politics Today na gidan talabijin din dangane da siyasar Najeriya yayin da ake tunkarar zaben 2027. Dandazon jama’a sun tarbi Gwamna Yusuf a Kano Jaridar ta rawaito cewa ko da ya.ke daga bisani Wike ya ce ba wai har…
Dubban al’ummar jihar Kano sun fito kan tituna a ranar Asabar domin tarbar Gwamna Abba Yusuf bayan dawowarsa daga Abuja, inda ya gana da shugabannin jam’iyyar APC. Rahotanni sun nuna cewa gwamnan ya kuma kasance cikin tawagar APC da ta je jihar Bauchi domin jawo Gwamna Bala Mohammed ya koma jam’iyyar daga PDP, duk da cewa har yanzu bai bayyana matsayinsa ba. Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano Tarbar ta biyo bayan sauye-sauyen siyasa a Kano, ciki har da ficewar Rabiu Musa Kwankwaso daga NNPP zuwa ADC tare da hadewa da…
A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA, ke fuskantar matsaloli wajen samun magunguna, duk da kasancewarsu cikin tsarin. Shirin kula da lafiya na Hukumar KACHMA tsari ne na taimakekeniya domin tallafawa masu rauni, musamman mata da tsofaffi, domin samun kulawa ta musamman. Rahotanni sun nuna cewa, matsalar gudanar da shirin ta fi shafar mata da tsofaffi marasa lafiya. Wakilanmu sun lura da cewa, matsalar ta fi k’amari a asibitin K’wararru na Asibitin Murtala Muhammad. Asibitin na daya daga cikin manyan asibitocin da ke karɓar dimbin…
Gwamnatin Jihar Kano ta tura dalibai 550 daga cibiyoyin ilimi tara domin taimakawa wajen faɗaɗa rajistar rajistar masu zaɓe CVR, a wani yunƙuri na ƙara ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya a faɗin jihar. Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya bayyana hakan yayin ƙaddamar da shirin a filin wasanni na Kofar Mata, inda ake gudanar da babban aikin rajistar masu zaɓe. Wannan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da Abbas Ibrahim, Shugaban Kwamitin Yaɗa Labarai, ya fitar a madadin Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Zaɓe na Jihar Kano. A cewar Waiya, an horas da…
