Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Kan Karbar Shagunan Mutane Na Kasuwar Gyadi-Gyadi Yar Kasuwa
Afrika

Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Shugaban Karamar Hukumar Tarauni Kan Karbar Shagunan Mutane Na Kasuwar Gyadi-Gyadi Yar Kasuwa

April 6, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260406 WA0040

Ya mai girma Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, Hon. Ahmad Sekure a matsayina na dan karamar hukumar Tarauni na rubuta wannan wasika ne saboda kira a gareka, a matsayin ka na shugaban al’umma wanda suka amince maka zama shugaban su domin suna da kyakkyawan yakinin cewa zaka musu adalci, kare rayuwar su, tallafa musu da ilimi da ayyukan yi.

‎Ina mai kira da jan hankali dangane da batun sauya fasalin daya daga cikin kasuwannin da suke karkashin kulawar karamar hukumar Tarauni wato kasuwar ‘Yar Kasuwa dake unguwar Gyadi-Gyadi kuma mazabar Gyadi-Gyadi Kudu wacce take mallakin daidaikun mutane ciki harda marayu da iyayensu suka mutu suka bar musu gado suke gudanar da kasuwanci a wannan kasuwa da cewa yunkurin da akeyi na sabunta kasuwar abune mai kyau. Amma saidai akwai bukatar duba na tsanaki wajen aiwatar da aikin. Dalili na kuwa anan shine.

‎1. RASHIN INGANTACCEN SHUGABANCI

‎Na Farko: Babu cikkakken hadin kai a cikin shugabancin kasuwar wanda yasa aka sami rabuwar kai tsakanin bangorori biyu (wadanda suka amince da kuma wadanda basu amince ba) saboda rashin samun cikkakken bayani dangane da yadda makomar mammalaka shagunan zai kasance.

‎2. BABU TAKARDAR YARJEJENIYA

‎Na Biyu: A cikin Korafe-korafe da akeyi wanda kasani akwai batu na rashin wata gamsasshiyar takarda daga karamar hukuma zuwa ga mammallaka shaguna kan cewa ga yadda yarjejeniya zata kasance. Sannan basuda masaniya akan kamfanin da zaiyi aikin, karamar hukuma ce kawai ta kawo shi ba tare da zama dasu ba (a cewar shugabancin kasuwar da suka amince da aikin)

‎3. BARAZANA GA MAMMALLAKA SHAGUNA

‎Na Uku: Wadanda aka wakilta su tattauna da masu shaguna suna musu barazanar cewa gwamnatin ka zata kwacewa duk wanda yaki amincewa da bukatar aikin.

‎4. RASHIN KYAKKYAWAN WAKILCIN MASU SHAGUNA

‎Na Hudu: Akwai har yanzu wadanda suke wakiltar masu shaguna ba tare sanin wasu daga cikin masu shagunan ba, wanda a bisa doka dole ne kowa yasan halin da ake ciki. (Wanda kuma kanada masaniya akan cewa akwai wadanda basu sani ba).

‎5. MAKOMAR MATASA SAMA DA 1000 DAKE SANA’A A KASUWAR

‎Na Biyar: Ka duba adadin matasan da suke neman abunci a cikin kasuwar wanda babu daya daga cikin su da gwamnati ta bawa aikin yi. Sune suka samarwa kansu mafita ba tare da tallafin gwamnati ba wanda sun haura akalla mutane 1000.

‎Saboda haka yakamata duk abunda za’ayi a duba maslahar al’umma domin saboda su aka samu damar kaiwa inda ake a halin yanzu. Kuma shugabanci yana dorewa ne kadai idan akwai adalci a cikin sa. Da fatan za’ayi nazari akan wannan muhimmin al’amari domin yin duba na tsanaki.

‎Nine naka

‎✍️ Musa Ado Musa

‎Mai Kishin Karamar Hukumar Tarauni

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.