Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎
Kano

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Northwest University (1)

‎Hukumar gudanarwar Jami’ar Northwest University Kano (NWUK) ta amince da korar dalibai 34 daga jami’ar bayan samunsu da hannu a laifukan da suka shafi satar amsa lokacin jarabawa.

‎Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Ibrahim ya sanya wa hannu a madadin Magatakardar jami’ar, Dr. Adm. Isyaku Adamu.

‎Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke wannan hukunci ne a yayin taron hukumar gudanarwar jami’ar karo na 66 da aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Yunin 2026, lokacin da ake nazarin sakamakon jarabawar zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2024/2025.

‎Ta ce an dauki matakin ne bisa tanade-tanaden dokokin gudanar da jarabawa da ke kunshe a cikin kundin dokokin dalibai na jami’ar.

‎Baya ga korar daliban 34, hukumar gudanarwar ta kuma amince da dakatar da wasu dalibai 18 daga karatu na wani lokaci saboda irin wadannan laifuka, yayin da aka bai wa dalibai 22 takardun gargadi kan laifukan da suka shafi jarabawa.

‎Hakazalika, sanarwar ta ce an wanke wata daliba mai suna Rukayya Ahmad Zukuri daga dukkan zarge-zargen da ake yi mata bayan sake duba lamarin.

‎Jami’ar ta sake jaddada kudirinta na tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin ilimi, tare da gargadin dalibai da su kiyaye dokoki da ka’idojin gudanar da jarabawa, tana mai cewa duk wanda aka samu da karya dokokin zai fuskanci hukuncin da ya dace.

Northwest
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026

NDLEA Ta Kone Tan 12.2 Na Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutum 

June 29, 2026

Ranar Yaƙi da Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya: Ƙungiyoyi Sun Yi Gangamin Wayar da Kai, Sun Nemi Haɗin Kan Al’umma Don Daƙile Shaye-shaye a Kano

June 26, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.