A Jihar Kano, an ƙaddamar da wani shiri na kwanaki shida na rajistar Katin zaɓe, a wani yunƙuri na ƙara yawan masu katin zaɓe da kuma ƙarfafa shiga harkokin dimokuraɗiyya. Shugaban Kwamitin Ƙarfafa Rajistar Masu Katin Zaɓe na jihar, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ne ya jagoranci ƙaddamar da shirin a ranar Laraba a cibiyar wasanni da ke Kofar Mata. A cewarsa, an tanadi rumfunan rajista guda 20 domin sauƙaƙa wa jama’a yin rajista cikin gaggawa da kuma rage cunkoso. Waiya ya bayyana gamsuwarsa kan yadda jama’a suka fito domin yin rajistar, yana mai cewa hakan na nuna fahimtar al’umma kan…
Author: Wafsym
Babban Bankin Najeriya CBN ya fitar da sunayen bankuna 33 da ya amince cewa jarinsu ya kai su ci gaba da gudanar da hada-hada a cikin ƙasar, a wani yunƙuri na kare dukiyoyin abokan hulɗarsu. Cikin wata sanarwa da CBN ya fitar a jiya Laraba, ya ce shirin wanda aka soma tun watan Maris na shekarar 2024, an kammala shi a yanzu bayan shafe watanni 24 ana yinsa, domin ƙarfafa tsarin hada-hadar kuɗi tsakanin bankuna da abokan hulɗarsu a Najeriya. Gawuna da Kwankwaso sun hade Babban bankin ya ce bankunan 33 da aka amince dasu sun samar da jari na…
Tsohon mataimakin gwamnan Kano kuma tsohon ɗan takarar gwamnan jihar a jam’iyyar APC ya karɓi katin jam’iyyar ADC a hukumance, a ranar Litinin. A ranar Lahadi ne ya sanar da ficewa daga jam’iyyar APC, tare da jadadda mubaya’arsa ga tsarin Kwankwasiyya. Gawuna Ya Fice Daga Jam’iyyar APC Bayanai na cewa komawar tasa na da alaƙa da rashin yadda ake zargin mayar da shi saniyar ware a jam’iyyar APC. Tundai bayan da kotun koli ta Najeriya ta tabbatar wa da Abba Kabir Yusuf kujerar gwamnan Kano, wasu magoya bayan Nasiru Gawuna suka yi ta sa ran shugaba Tinubu zai bai wa…
Tsohon mataimakin gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC). A cikin wata takardar murabus mai ɗauke da kwanan watan 29 ga Maris, 2026, wadda ya aikewa shugaban jam’iyyar a mazabarsa ta Gawuna da ke karamar hukumar Nassarawa, Gawuna ya ce matakin da ya dauka na barin jam’iyyar na son rai ne kuma na kashin kansa. Gawuna ya sauka daga shugabancin kwamitin Gudanarwa na Bankin Lamuni na Tarayya. Ya bayyana a cikin takardar cewa: “Ina sanar da ku a hukumance cewa na fice daga jam’iyyar APC daga ranar 29 ga Maris, 2026.”…
Gawuna ya sauka daga shugabancin kwamitin Gudanarwa na Bankin Lamuni na Tarayya. Gawuna ya ce murabus ɗin nasa ya fara aiki nan take, kuma ya yi dai-dai da umarnin shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na cewa duk masu riƙe da mukaman siyasa su sauka gabanin wasu harkokin siyasa. Ya godewa shugaban Ƙasa bisa damar da aka ba shi na yin aiki, inda ya bayyana cewa hakan wata babbar dama ce. Rahotanni sun kuma nuna cewa Gawuna na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC, yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen siyasa gabanin zaɓen 2027.
Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta Jihar Kano, ta koka a kan sama da faɗi da ake yi da madarar tamowa ta ƙananan yara masu larurar rashin abinci mai gina jiki tare da handame jakunkunan ɗalibai da ke yankunan ƙananan hukumomi 44 na faɗin jihar. A bisa haka gwamnatin, ta gindaya doka da oda mai ƙarfi ga dukkan waɗanda suke da alhaki wajen karkatar da irin waɗannan muhimman kayayyakin tagomashin inganta rayuwar al’umar dake kafatanin jihar. Jami’in Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa Reshen jihar Kano, Malam Balarabe Yusuf Sani, ya nuna damuwa bisa yadda rashin gaskiya da amana suka mamaye…
Sheikh Dr. Isa Pantami ya buƙaci Malam Nasir El-Rufai da abokan siyasarsa su ajiye saɓanin da ke tsakaninsu, ya yi wannan kiran ne a makabarta yayin binne mahaifiyar El-Rufai, Hajiya Umma, a Abuja. Pantami ya yi wannan kira ne a huɗubarsa a maƙabartar Gudu ranar Lahadi. Ya roƙi shugabanni su fifita haɗin kai tare da tunawa da alherin da suka yi wa juna. Ya jaddada cewa rayuwa mai wucewa ce kuma dole kowa ya bar duniya wata rana. Ya ƙara da cewa nasara na zuwa ne ta bin hanyar Allah ba dabarun siyasa ba. A wurin jana’izar, manyan ‘yan siyasa…
Hukumar Shirya Jarabawar Ƙasashen Yammacin Afirka, West African Examinations Council (WAEC), ta bayyana cewa an gudanar da jarabawar ta a cibiyoyi 166 a faɗin Najeriya tsakanin ranar 28 ga Janairu zuwa 14 ga Fabrairu, 2026. A cikin sanarwar da mukaddashin shugaban hulɗa da jama’a na hukumar, Moyosola F. Adesina, ya fitar daga hedikwatar WAEC da ke Yaba, an ce jimillar ɗalibai 10,480 ne suka zauna jarabawar. 2026: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na kwamfuta Daga cikin wannan adadi, ɗalibai 3,429, wanda ya kai kashi 32.72 cikin ɗari, sun samu sakamakon credit a aƙalla darussa biyar ciki har da…
Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar ADC a ranar Litinin a hukumance. Tsohon Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Kano wanda yake na hannun daman Kwankwaso, Yusuf Kofar Mata ne, ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta. Mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo yayi murabus A saƙon da ya wallafa ya gayyaci jama’a su halarci gidan jagoran Kwankwasiyya da ke Miller Road a unguwar Bompai da ke Kano da misalin ƙarfe 12 na rana. Wannan sanarwa…
Mataimakin gwamnan jihar Kano Arewa maso Yammacin Najeriya karkashin inuwar jam’iyyar NNPP Aminu Abdussalam Gwarzo yayi murabus. A cewar kafar yada labaran Arewa Updates wannan na cikin sanarwar da mai magana da yawun ƙungiyar Kwankwasiya Dakta Habibu Sale Mohammed ya fitar. Hisbah ta kama wasu matasa a otel a Kano Sanarwar ta bayyana cewa an ɗauki matakin ne domin tabbatar da zaman lafiya da kuma bai wa ofishin damar gudanar da aikinsa yadda ya kamata ba tare da tangarda ba. Sanarwar ta ce murabus ɗin ba yana nufin amincewa da zarge-zargen da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta yi ba, inda…
