Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » 2026: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na kwamfuta
Afrika

2026: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na kwamfuta

March 29, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
WAEC Exams

Hukumar Shirya Jarabawar Ƙasashen Yammacin Afirka, West African Examinations Council (WAEC), ta bayyana cewa an gudanar da jarabawar ta a cibiyoyi 166 a faɗin Najeriya tsakanin ranar 28 ga Janairu zuwa 14 ga Fabrairu, 2026.

A cikin sanarwar da mukaddashin shugaban hulɗa da jama’a na hukumar, Moyosola F. Adesina, ya fitar daga hedikwatar WAEC da ke Yaba, an ce jimillar ɗalibai 10,480 ne suka zauna jarabawar.

2026: WAEC ta fitar da sakamakon jarrabawar WASSCE na kwamfuta

Daga cikin wannan adadi, ɗalibai 3,429, wanda ya kai kashi 32.72 cikin ɗari, sun samu sakamakon credit a aƙalla darussa biyar ciki har da Turanci da Lissafi—abin da ke nuna ƙaruwa da kashi 5.76 idan aka kwatanta da sakamakon shekarar 2025 da ya tsaya a kashi 26.96.

Hukumar ta kuma bayyana cewa ɗalibai 43 masu buƙata ta musamman sun shiga jarabawar, inda aka ba da kulawa ta musamman ga makafi 11, masu matsalar ji guda 4, da kuma albinos guda 4, a wani yunƙuri na tabbatar da daidaito a fannin ilimi.

Dangane da sakamakon, WAEC ta ce an riga an kammala duba sakamakon ɗalibai 8,418, wanda ya kai kashi 80.32 cikin ɗari, yayin da sakamakon ɗalibai 2,062 ke ci gaba da dubawa sakamakon wasu kurakurai da aka gano daga ɓangaren ɗaliban.

Sai dai hukumar ta riƙe sakamakon ɗalibai 75 bisa zargin hannu a magudin jarabawa, inda ta ce ana ci gaba da bincike kafin ɗaukar matakin da ya dace.

A ƙarshe, WAEC ta shawarci ɗalibai da su duba sakamakonsu ta shafin yanar gizon hukumar, inda kuma za su iya sauke kwafin takardar shaidarsu ta dijital cikin sauƙi.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.