Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP a zaɓen 2023, Rabiu Musa Kwankwaso, zai koma jam’iyyar ADC a ranar Litinin a hukumance.
Tsohon Kwamishinan Ilimi Mai Zurfi na Jihar Kano wanda yake na hannun daman Kwankwaso, Yusuf Kofar Mata ne, ya tabbatar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta.
Mataimakin gwamnan Kano Aminu Abdussalam Gwarzo yayi murabus
A saƙon da ya wallafa ya gayyaci jama’a su halarci gidan jagoran Kwankwasiyya da ke Miller Road a unguwar Bompai da ke Kano da misalin ƙarfe 12 na rana.
Wannan sanarwa ta tabbatar da jita-jitar da ake yi na cewar Kwankwaso na shirin ficewa daga jam’iyyar NNPP.
A baya-bayan nan, Kwankwaso ya fara tattaunawa da shugabannin ADC a Abuja da Kano.
An kuma ruwaito cewa ya gana da manyan jiga-gigan jam’iyyar, lamarin da ya sa ake tunanin yin haɗaka tsakanin jam’iyyun gabanin zaɓen 2027.
Ƙungiyar Kwankwasiyya, wadda ke da ɗimbin magoya baya a Kano, ana ganin ƙungiya ce mai ƙarfi da kowa zai so yin haɗakar siyasa da ita.
Masu sharhi kan al’amuran siyasa sun ce wannan mataki na iya rusa jam’iyyar NNPP, wadda ta yi fice ne saboda tasirin siyasar Kwankwaso.
Haka kuma suna ganin komawarsa ADC zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi, musamman idan wasu ’yan siyasa suka mara masa baya.
Yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa, ana ganin taron na ranar Litinin, zai iya buɗe wani sabon shafi a alƙiblar siyasar Kwankwaso.

