Yayin da ake cika shekaru 12 cif-cif da sace ƴan matan makarantar garin Chibok su 272 da ƙungiyar Boko Haram ta yi a shekarar 2014, masu fafutukar ganin an saki ƴan matan da ake kira da “BringBackOurGirls” suna neman amsa dangane da inda ragowar ƴan matan suke. Aƙalla ƴan mata 187 ne aka ceto ko kuma suka tsere daga hannun waɗanda suka sace su, inda har yanzu ba a san makomar ƴan matan guda 83 ba. Wannan ne ya sa ƙungiyar ta BringBackOurGirls ke neman sanin a halin da suke ciki. A watan sanarwa da ƙungiyar ta fitar ta zayyana…
Author: Wafsym
Tsagin jam’iyyar ADC da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark ke jagoranta, ya kori Nafiu Bala, wanda ake kallonsa a matsayin shugaban wani bangare na jam’iyyar, bisa zargin aikata ayyukan da suka sabawa manufofin jam’iyya. Haka kuma jam’iyyar ta kori wasu jiga-jigai da suka hada da ɗan majalisar wakilai Leke Abejide, da Kingsley Temitope, Obinna Norman, Kennedy Odiong, da Stella Chukwuma. Sanata mai wakiltar Adamawa ta Kudu, Binos Yaroe, ne ya gabatar da kudirin korar mambobin a ranar Talata yayin babban taron jam’iyyar na kasa da aka gudanar a Abuja, inda wakilai suka amince da kudirin ta hanyar kada kuri’ar…
Tsohon Ministan Sadarwa , Farfesa Isa-Ali Pantami, ya bayyana cewa ya kamata masu rike da mukaman gwamnati su gabatar da sahihan bayanai da ke nuna irin ayyukan da suka yi, yana mai jaddada cewa tsabtataccen tarihinsa bayan barin mulki ya isa shaida. Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a jihar Gombe yayin kaddamar da wani kundin bayanai da ke tattara manyan ayyuka guda 241 da kuma samar da damar ayyukan yi sama da 700 da aka aiwatar a lokacin mulkinsa. An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo …
Rundunar yansanda ta jihar Edo ta kama wasu gungun ɓatagari da su ka haɗa da jami’an ƴansanda biyar da gida ɗaya da aka kora daga aiki, tare da wasu mutum uku, bisa zargin cin zarafi, sace mutane da kuma kwace musu kudade a jihar. Jami’an da aka kama sun hada da ASP Bonny Paul Onajite, Insifekta Ehubarieme Wisdom, Insifekta Arebame Godspower, Kofur Mordi Philip, Kofur Okon Elvis, da kuma Destiny Emmanuel wanda aka kora daga aikin dan sanda. Rahoton Daily Trust ya ce sauran wadanda aka kama tare da jami’an sun hada da Goodluck Jaja, mai sana’ar POS, da Samuel…
Manchester City ta ƙara rage yawan makin da ke tsakaninta da Arsenal bayan nasarar da ta samu a wasan da ta fafata da Chelsea. Manchester City ta yi nasara kan Chelsea da ci 0-3 a filin wasa na Stamford Bridge. Yanzu Manchester City tana da maki 64 a matsayi na biyu, bayan Arsenal da ke ta ɗaya da maki 70. City na da wasa guda kwantai da Crystal Palace, wanda aka ɗaga yin shi saboda dalilai a baya, idan City ta ci wasan zai zama saura maki 3 kacal tsakaninta da Arsenal. A yanzu haka kuma a makon gobe ne…
Wani mummunan lamari ya auku a kan iyakar Jihar Borno da Jihar Yobe, inda rahotanni ke cewa wani hari daga sama da sojoji suka kai ya fada kan wata kasuwa ta al’umma, lamarin da ake fargabar ya hallaka fiye da mutane 50. Bisa ga bayanan da ke fitowa a hankali, an ce harin ya faru ne yayin wani samame da ake kai wa ‘yan tada kayar baya a yankin Arewa maso Gabas. Sai dai abin takaici, fararen hula sun tsinci kansu a cikin harin, wanda ya jawo asarar rayuka da raunuka masu yawa INEC ta ɗage aikin sabunta bayanan rajistar…
Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da ɗage aikin sabunta rajistar masu zaɓe da ta shirya yi a duk faɗin ƙasar nan zuwa bayan babban zaɓen shekarar 2027 kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito. An yanke wannan shawara ne bayan wani taro da hukumar ta gudanar da Kwamishinonin Zaɓe na jihohi, inda aka tattauna muhimman batutuwan da suka shafi zaɓe. Gwamnan Kano ya naɗa Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jiha A wata sanarwa da Kwamishinan ƙasa kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai da wayar da kan masu zaɓe, Mohammed Haruna, ya fitar, ya ce…
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya naɗa Hajiya Bilkisu Maimota a matsayin shugabar ma’aikata ta jihar ta dindindin. Wannan na kunshe a wata samarwa da babban sakataren yaɗa labarai na gwamnan Kano,. Mustapha Muhammad ya fitar,.inda ya ce gwamnan ya sanar da haka ne a wajen bikin biyan ƴan fansho hakkunan su, karo na shida. Harin masu iƙirarin jihadi ‘ya kashe wani babban jami’in soja’ a jihar Borno Ya ce tabbatar da Maimota a wannan lokacin ya yi daidai domin samun cigaba wajen gudanar da aikin gwamnati. Inda ya ce an tabbatar da Maimota ne bayan ta rike matsayin…
Wani jami’i a jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ce an kashe wani babban jami’in soja a wani hari da masu iƙirarin jihadi suka kai kan sansanin soji. Shugaban ƙaramar hukumar Kaga ya ce Birgediya Janar O. O. Braimah ya rasu ne bayan da ‘yan ta’addan suka kai hari sansanin da ke Benisheikh cikin dare. Shugaban INEC ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai Wannan ne karo na biyu da aka kashe janar ɗin Soji a arewacin Najeriya cikin ƴan watannin da suka gabata. Rahotanni sun ce wasu jami’an tsaro, da na rundunar tsaro JTF, da kuma wasu…
Ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja babban birnin tarayyar Najeriya, ya sanar da soke duk wasu buƙatun neman biza da aka shigar. Ta buƙaci masu neman shiga ƙasarta su duba saƙonninsu na imel don samun cikakkun bayanai kan mataki na gaba. Shugaban INEC ya ja kunnen kafafen yaɗa labarai A wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ofishin Jakadancin Amurkar ya ce za a ci gaba da gudanar da tantance neman bizar a ofishin jakadancinta da ke Legas. Sanarwar ta ce jami’anta za su ci gaba da duba bayanan ƴan Amurka ne kawai a yanzu musamman ga masu buƙatar…
