Kwamitin Kartakwana a kan Katin Zaɓe (CVR) a Jihar Kano ya buƙaci limaman masallatan Juma’a da su ƙara himma wajen wayar da kan al’umma kan muhimmancin mallakar katin zaɓe da kuma shiga cikin harkokin dimokuraɗiyya. Wannan kira ya fito ne yayin wata ganawa da kwamitin ya yi da limaman masallatan Juma’a, inda Shugaban Ƙaramin Kwamitin Hulɗa da Malamai, Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa, ya jaddada muhimmancin rawar da malamai ke takawa wajen isar da saƙonnin da suka shafi ci gaban al’umma. Sheikh Ibrahim Abubakar Tofa ya bayyana cewa malamai na da tasiri mai girma a cikin al’umma, don haka haɗin gwiwarsu…
Author: Wafsym
Rahotanni sun bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwar man fetur kuma hamshaƙin mai zuba jari a harkar gidaje da kadarori a jihar Kano, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manager. Kano Tourism Information Ɗa ga marigayin mai suna Surajo Audu Manager, ne ya tabbatar da rasuwar mahaifin nasa ga jaridar Daily Nigerian, inda ya bayyana cewa ya rasu ne a yau Laraba a wani Asibiti mai suna Saudi German Hospital Cairo da ke birnin Cairo bayan fama da doguwar rashin lafiya. Marigayin ya kasance ɗaya daga cikin manyan ƴan kasuwa a Jihar Kano, inda ya yi fice a…
Rikicin da ke girgiza kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ya kamata ya zama lokaci na zurfin tunani ga shugabannin Arewa maimakon ci gaba da fafutukar neman iko. An kafa ACF ne domin hada kan Arewacin Najeriya, kare muradunta, inganta zaman lafiya, da bayar da jagoranci kan al’amuran da suka shafi yankin. Idan rikice rikicen cikin gida suka rikide zuwa zarge zargen cin hanci, killace ofisoshi da ‘yan sanda, da rudanin kundin tsarin mulki, to martabar Arewa gaba daya ce ke tabarbarewa a idanun kasa baki daya. Abin da ya fara a matsayin sabani tsakanin Kwamitin zartarwa a matakin kasa da…
Ƙasar Koriya ta Kudu ta bayyana cewa za ta mayar da martani kan harin da aka kai wa wani jirgin dakon kaya mallakin kamfanin ƙasarta a Tekun Fasha, bayan bincikenta ya gano waɗanda ke da hannu a harin. A cikin wata sanarwa da Koriya ta Kudu ta fitar, gwamnatin ƙasar ta yi Allah-wadai da harin tare da cewa tana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin. Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa ƙwararrun Koriya ta Kudu sun gudanar da binciken farko domin tantance irin ɓarnar da…
Tsohon ministan sadarwa na Najeriya Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ƙarin haske kan dalilin da ya sa ya taɓa mayar da akwatin zaɓensa zuwa Abuja daga Gombe. A hirarsa da gidan talabijin na TVC a yau Lahadi, Pantami wanda ɗaya ne daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027, ya kuma yi tsokaci kan zargin da ake masa na watsi da lamuran jam’iyyar ta APC na tsawon lokaci. Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya Pantami ya ce ya maida akwatin zaɓensa zuwa Abuja ne a shekarar 2019 saboda muƙamin da ya riƙe…
Attajirin ɗan kasuwar Najeriya kuma hamshaƙin mai kuɗi a Afirka, Aliko Dangote, na duba yiwuwar gina sabuwar matatar mai mai ƙarfin tace ganga dubu 650 a kullum a ƙasar Kenya kamar yadda TRT Afrika ta rawaito. Rahotanni sun ce Dangote ya fi karkata wajen gina matatar a birnin Mombasa saboda tashar jirgin ruwanta mai girma da zurfi. Ya kuma bayyana cewa tattalin arzikin Kenya ya fi girma a yankin Gabashin Afirka, tare da yawan masu amfani da albarkatun mai. Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano Dangote ya ce komai…
Daga Comrade Abbas Ibrahim Yayin da Jihar Kano ke tunkarar wani muhimmin mataki a harkokin siyasa na Babban Zaɓen 2027, bukatar daukar matakan da suka dace domin kare rayuka, dukiyoyi da martabar dimokuradiyya na kara zama wajibi fiye da kowane lokaci. Haramta daukar makamai a wuraren tarukan siyasa ba zabin son rai ba ne, wajibi ne. Rikicin da ya faru a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, a kusa da kasuwar Farm Centre dake Kano, ya sake fito da yadda tarukan siyasa ke iya rikidewa zuwa tashin hankali idan aka bar magoya baya ba tare da kulawa da takunkumi ba.…
Tsohon ministan sadarwa, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya yi watsi da abin da ya kira “naɗin sarauta” da ake yi wa wasu yan takara a matsayin maslaha a dukkan kujerun zaɓe a jihar Gombe. A wata sanarwa da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin mambobi da magoya bayan ƙungiyar Pantamiyya Movement, ya ce babu ingantacciyyar maslaha a doka matuƙar ba a haɗa dukkan yan takarar da suka sayi fom ɗin tsayawa takara ba. HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim Sanarwar ta ce dokar zaɓe ta ƙasa ta…
Tsohon ɗantakarar shugaban Najeriya a zaɓen 2023 Peter Obi, da tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun koma jam’iyar NDC. Jiga-jigan adawar sun karɓi katin jam’iyar ne bayan ficewa daga jam’iyar ADC saboda rikice-rikicen shugabanci da suka ce sun dabaibaye ta. HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim Dukkansu sun karɓi katin NDC ne a hedikwatar jam’iyar tare da jagoranta Hon. Seriake Dickson. Ana ta hasashen cewa jiga-jigan adawar na son yin takarar shugaban ƙasa da mataimaki, inda magoya bayansu suka ƙaddamar da wata tafiya da suka kira da…
Harin da wasu da ake zargin ’yan daba masu alaƙa da siyasa suka kai Kasuwar Siyar Da Wayoyi Ta Farm Cente da ke Kano ya janyo hankalin jama’a, inda ake ganin lamarin wata babbar barazana ce ga zaman lafiya da ci gaban tattalin arziki a jihar, musamman yayin da ake tunkarar zaɓen 2027. Lamarin ya faru ne a ranar Litinin, 27 ga Afrilu, 2026, inda aka ga yadda wasu suka mamaye kasuwar, suka yi sace-sace, tare da lalata dukiyoyi ciki har da motoci da babura. Haka kuma, mutane da dama sun samu raunuka a yayin harin Kasuwar Farm Centre na…
