Author: Wafsym

Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye Kwamitin Hadin Gwiwar Hukumomi na Jihar Kano kan Yaki da Shan Miyagun Kwayoyi da Fataucin Haramtattun Abubuwa ya samu nasarar gurfanar da wasu mutane biyu tare da tabbatar da hukuncin dauri shekara Tara (9) a kansu bisa laifin samar da sinadarin solisho da wasu abubuwa masu sanya maye ga yara. Hukuncin ya zama gargaɗi mai ƙarfi ga duk wanda ke cin gajiyar raunanan yara tare da jefa su cikin haɗarin shan abubuwan maye, cewa za su fuskanci cikakken hukuncin da doka ta tanada.…

Read More

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar Labour Party (LP), Alhaji Hamisu Santuraki, ya yi alkawarin kafa Hukumar Kula da Hayar Gida da ’Yan Hayar Gida, idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027. Santuraki ya ce manufar hukumar ita ce dakile ƙarin kuɗin haya ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare ’yan haya daga cin zarafi da sauran matsalolin da suka shafi haya. Ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa, Comrade Abbas Ibrahim, inda ya ce hukumar ba za ta sanya farashin haya iri ɗaya ga dukkan gidaje ba, sai dai ta tsara farashi bisa la’akari da wurin da gida…

Read More

Ɗan takarar mataimakin gwamnan Jihar Kano na Jam’iyyar Labour Party (LP), Kwamared Abbas Ibrahim, ya bayyana rasuwar Babban Sakataren Ƙungiyar Ƙwadago ta Najeriya (NLC), Kwamared Emmanuel Ugboaja, a matsayin babban rashi ga ƙungiyar ƙwadago da ma Najeriya baki ɗaya. A cikin saƙon ta’aziyyar da ya aike wa Shugaban NLC, Kwamared Joe Ajaero, ranar 27 ga Agusta, 2026, Abbas ya ce rasuwar Ugboaja ta girgiza harkar ƙwadago, duba da irin gudunmawar da marigayin ya bayar wajen kare haƙƙin ma’aikata da inganta walwalarsu. Ya ce marigayin ya kasance jagora mai hangen nesa wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen tabbatar da adalci da…

Read More

Kano PHCMB Ta Ƙara Ƙaimi Wajen Jawo Al’umma Zuwa Ayyukan Lafiya Hukumar Kula da Ayyukan Kiwon Lafiya Matakin Farko ta Jihar Kano (KSPHCMB) ta ce za ta ƙara mayar da hankali wajen ƙarfafa hulɗa da al’umma domin ƙara yawan masu amfani da ayyukan kiwon lafiya matakin farko a jihar. Hukumar ta bayyana hakan ne a ranar Talata, yayin wani taron haɗin gwiwa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a zauren taron hukumar da ke Kano. Taron ya samu halartar masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na jihar, inda aka duba yadda ayyukan hulɗa da…

Read More

Allah Ya yi wa Alhaji Sani Gwarzo, wanda aka fi sani da “Tumbuleke”, rasuwa. Alhaji Sani Gwarzo ya rasu ne a yau Talata, a Asibitin Barau Dikko da ke Kaduna, bayan fama da rashin lafiya. Labarin rasuwar marigayin ya jefa ’yan uwa, abokan rziki da sauran masoyansa cikin jimami da alhini. Alhaji Sani Gwarzo ya kasance mutum da mutane da dama suka san shi, kuma rasuwarsa ta haifar da babban gibi ga iyalansa da wadanda suka san shi. A wannan lokaci na alhini, muna mika sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin, ’yan uwa da abokan arziki. Muna rokon Allah Maɗaukakin Sarki…

Read More

Shugaban Rundunar Haɗin Gwiwa ta Jihar Kano kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Safararsu (MATFDAT), Alhaji Muhyi Magaji Rimin Gado, ya bayyana cewa babu wani mutum ko wata hukuma da za a yi wa rangwame a yaƙin da ake yi da miyagun ƙwayoyi a jihar. ‎Muhyi Magaji ya bayyana hakan ne yayin wani shirin DuniyarMu a Yau, wanda Freedom Radio Kano, inda ya ce duk wanda aka samu yana safarar, sayarwa ko aikata wani laifi da ya shafi miyagun ƙwayoyi zai fuskanci hukunci kamar yadda doka ta tanada. ‎Ya ce rundunar ta riga ta kai wasu daga cikin waɗanda…

Read More

Ƙungiyar Good Governance Development Analyst Association (GGODAA) ta gargadi ’yan siyasa da su guji amfani da kalaman ƙiyayya, cin mutunci da tunzura jama’a yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027. Shugaban ƙungiyar, Alkali Sidi Bello, Esq., ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, 9 ga Agusta 2026, inda ya ce ya kamata ’yan takara su mayar da hankali kan manufofi, shirye-shirye da hangen nesansu, maimakon amfani da ƙabila, addini ko yanki wajen raba kan al’umma. GGODAA ta ce kalaman ƙiyayya da tunzura jama’a na iya haifar da tashin hankali da barazana ga zaman lafiyar…

Read More

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da Kwamitin Haɗin Gwiwa na Hukumomi kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi, tare da sanya hannu kan Dokar Zartarwa da za ta ƙarfafa yaƙi da daba da sauran ayyukan ta’addanci a faɗin jihar. Mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba. Sakamakon Binciken Jami’ar Northwest Kano Ya Haskaka Matsalolin Lafiyar Al’umma a Tofa Gwamna Abba ya ce shan miyagun ƙwayoyi na daga cikin manyan matsalolin da ke addabar matasan Kano, yana mai cewa matsalar tana haddasa…

Read More

Jami’ar Northwest Kano ta gabatar da sakamakon binciken lafiyar al’umma (Community Diagnosis) da ɗaliban fannin Likitanci (MBBS) suka gudanar a Unguwar Doka da ke Ƙaramar Hukumar Tofa ta Jihar Kano, domin taimakawa wajen inganta tsare-tsaren kiwon lafiya da ayyukan kula da lafiyar al’umma. An gabatar da sakamakon binciken ne a wani taro da Sashen Kiwon Lafiyar Al’umma na Tsangayar Kimiyyar Asibiti, ƙarƙashin Kwalejin Kimiyyar Lafiya ta jami’ar, ya shirya bayan kammala zangon aikin koyon aiki na uku na ɗaliban MBBS. Da yake jawabi a madadin Mataimakiyar Shugabar Jami’ar, Farfesa Amina Salihi Bayero, Bursar na jami’ar, Malam Salmanu Muhammad Kibiya, ya…

Read More

Rikicin da ya shafi bayar da shaidar zama ɗan ƙasa a Ƙaramar Hukumar Jos North ta Jihar Filato ya ɗauki sabon salo, bayan da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jos North, ƙarƙashin jagorancin Ujah Anaguta, Mai Martaba Pozoh Johnson, tare da Ƙungiyar Cigaban Anaguta (Anaguta Development Association) da wasu ƙungiyoyi suka nemi Babbar Kotun Jihar Filato ta ba su damar shiga cikin shari’ar da ke tsakanin Fatima Baba Akawu da Ƙaramar Hukumar Jos North. A zaman kotun da aka gudanar ranar Juma’a, lauyoyin ɓangarorin biyu sun yi muhawara kan buƙatar masu neman shiga cikin shari’ar. Lauyoyin nasu sun ƙalubalanci halascin bayyanar…

Read More