Author: Wafsym

Mai Martaba Sarkin Gaya, Dakta Ali Ibrahim Abdulkadir, ya yi kira ga al’ummar Masarautar Gaya da su rungumi rajistar katin zaɓe tare da tabbatar da mallakarsa, yana mai jaddada cewa katin zaɓe shi ne ginshiƙin dimokuraɗiyya kuma hanya mafi inganci ta zaɓen shugabanni nagari. Sarkin ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Ƙaramin Kwamitin Kartakwana kan Rajistar Katin Zaɓe (CVR) na Ɗan Malikin Kano, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai, wanda ya jagoranci tawagar kwamitin zuwa masarautar domin wayar da kan jama’a kan muhimmancin katin zaɓe. Tun da farko, Kwamared Auwalu Mudi Yakasai ya ce kwamitin ya samu gagarumin…

Read More

Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), Kwamared Alhassan Yahya, ya buƙaci ‘yan jaridun yanar gizo da su ba da fifiko ga gaskiya, sahihancin labarai da bin ƙa’idojin aikin jarida, yana mai jaddada cewa amincewar jama’a ba ta ginu ne kan saurin wallafa labari ba, illa ingancinsa da gaskiyarsa. Shugaban na NUJ ya bayyana haka ne a jawabin da Kwamared Abbas Ibrahim, Amintaccen Ɗan Kwamitin Amintattu na Ƙasa mai kula da Shiyya ta A, ya gabatar a madadinsa yayin bikin ƙaddamar da Online Chapel na NUJ reshen Jihar Jigawa, wanda aka gudanar ranar Talata a Cibiyar ‘Yan Jarida ta NUJ…

Read More

Gwamnatin tarayya ta yi umarnin sauya tsarin karatu a Najeriya, sakamakon gano cewa fiye da yara miliyan 20 ƴan makarantar firamare sunabarin makarantar tun kafin su kai ga matakin sikandire. Ministan ilimi, Dakta Tunji Alausa, shi ne ya bayyana hakan a yau Talata, a wajen ƙaddamar da kwamitin sanya idanu na ma’aikatar shirin ilimin bai ɗaya na ƙasa a birnin tarayya Abuja. Jaridar Blueprint ta ruwaito cewa Najeriya dai tana gudanar da tsarin ilimi na shekaru 6-3-3-4, wanda ya ƙunshi shekaru shida na firamare, shekaru uku a ƙaramar sikandire, shekaru uku a babbar sikandire, sai kuma ma fi ƙarancin shekaru…

Read More

‎Hukumar gudanarwar Jami’ar Northwest University Kano (NWUK) ta amince da korar dalibai 34 daga jami’ar bayan samunsu da hannu a laifukan da suka shafi satar amsa lokacin jarabawa. ‎Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Abubakar Ibrahim ya sanya wa hannu a madadin Magatakardar jami’ar, Dr. Adm. Isyaku Adamu. ‎Sanarwar ta bayyana cewa, an yanke wannan hukunci ne a yayin taron hukumar gudanarwar jami’ar karo na 66 da aka gudanar a ranakun 17 da 18 ga watan Yunin 2026, lokacin da ake nazarin sakamakon jarabawar zangon karatu na biyu na shekarar karatu ta 2024/2025. ‎Ta ce an dauki matakin…

Read More

The Senate of Northwest University Kano (NWUK) has approved the expulsion of 34 students for their involvement in examination malpractice. The decision was announced in a statement signed by Abubakar Ibrahim on behalf of the Registrar, Dr. Adm. Isyaku Adamu. Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎ According to the statement, the decision was reached during the University’s 66th Regular Senate Meeting, held on Wednesday, June 17, and Thursday, June 18, 2026, while considering the Second Semester 2024/2025 examination results. The disciplinary action was taken in line with the…

Read More

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana aniyarta ta ƙara bai wa Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Kasa (NDLEA) tallafi, ciki har da samar da ƙarin motocin aiki, domin ƙarfafa yaƙi da safara da kuma ta’ammali da miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar. ‎Wannan na ƙunshe ne a saƙon Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Faruq Ibrahim, ya gabatar yayin bikin ƙona fiye da tan 12 na miyagun ƙwayoyin da aka ƙwace bayan kotu ta ba da umarnin lalata su. ‎An gudanar da bikin ne a yankin Kalebawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin…

Read More

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) ta kone tan 12.2 na miyagun ƙwayoyi da haramtattun magunguna da ta ƙwace daga hannun masu safara a Jihar Kano, yayin da ta bayyana cewa ta kama mutum 904 bisa laifukan da suka shafi miyagun ƙwayoyi tsakanin watan Janairu da Yunin 2026. An gudanar da aikin kone ƙwayoyin ne a ranar Litinin a Kano, inda Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar, Alhaji Umar Ibrahim Faroukh, ya wakilta, ya sake jaddada aniyar gwamnatin jihar na ci gaba da yaƙi da shaye-shaye da duk wani nau’in laifi.…

Read More

Ƙungiyoyin farar hula masu yaƙi da sha da fataucin miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano sun yi kira ga gwamnati, iyaye, malamai da sauran masu ruwa da tsaki da su haɗa kai domin daƙile matsalar shaye-shaye, wadda suka bayyana a matsayin babbar barazana ga makomar matasa da ci gaban al’umma. An bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin gangamin wayar da kai na “My Voice Against Drugs Walk”, da aka shirya domin bikin Ranar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Duniya, ranar da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN) ta ware a duk shekara domin wayar da kan al’umma kan illolin…

Read More

Daga Abbas Ibrahim Kafa Kwamitin Musamman Kan Yaƙi da Shan Miyagun Ƙwayoyi da Fataucin Su da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya yi, na ɗaya daga cikin matakan da suka zo a daidai lokacin da jihar ke ƙara fuskantar barazanar  shaye-shaye da fataucin miyagun ƙwayoyi ke yi ga tsaro, lafiya da makomar matasa. A tsawon shekaru, Kano na ci gaba da fama da matsalar shan miyagun ƙwayoyi, musamman a tsakanin matasa. Duk da irin muhimmancin da jihar ke da shi a matsayin cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya, hakan ya kuma sa ta kasance cikin wuraren da masu safarar miyagun…

Read More