Author: Wafsym

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka a Jihar Kano na da alaƙa da shan miyagun ƙwayoyi da fataucinsu, lamarin da ya nuna yadda matsalar ke da nasaba da rikice-rikicen daba da a yankin. Rahoton sirri da aka samu ya nuna cewa shan miyagun ƙwayoyi ya zama babban abin da ke ƙarfafa ƙungiyoyin daba, waɗanda ke shiga rikice-rikicen tashin hankali, hare-haren makamai da faɗace-faɗacen titi a sassan jihar. Rahotan, wanda rundunar ‘yansandan Jihar Kano ta tattara ƙarƙashin jagorancin kwamishinan ‘yansanda Ibrahim Adamu Bakori, ta nuna cewa an kama mutane 3,081 da ake…

Read More

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya kuma Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya soki yadda gwamnati ke ci gaba da karɓar bashi duk da cire tallafin man fetur a ƙasar. Sanusi ya bayyana hakan ne a wani taron shekara-shekara na The Niche Annual Lecture 2026 da aka gudanar a Legas, inda ya ce bai dace a dena bada tallafin mai ba amma a ci gaba da karɓar bashi ba tare da ganin amfanin hakan ba. An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje Ya ce cire tallafin ya zama dole saboda tsadar da yake haifarwa, tare da…

Read More

Majalisar Dattijan Najeriya ta tabbatar da naɗin Dakta Muttaqha Rabe Darma a matsayin ministan gidaje. Hakan ya biyo wasiƙar da shugaba Bola Tinubu ya aike wa Majalisar a Jiya, yana buƙatar ta amince da naɗin. A yayin zaman majalisar, wadda Shugaban majalisar Godswill Akpabio ya jagoranta, ƴan majalisar sun yi wa Dr Darma tambayoyi da dama kan dabarun da zai yi amfani da su wajen magance matsalar ƙarancin gidaje da ƙasar ke fama da ita. Bayan gamsuwa da amsoshin sa, Majalisar ta amince da naɗa shi. A ranar 21 ga watan Afrilun 2026 ne Shugaba Tinubu ya yi wasu sauye-sauye…

Read More

Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci gwamnatin ƙasar ta duba yiwuwar dakatar da yaƙin neman zaɓen 2027 a wasu jihohin arewa guda takwas da ke fama da matsalar tsaro. Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya Abdul Ningi ne ya gabatar da ƙudurin a zaman majalisar na ranar Alhamis, inda ya ce akwai buƙatar a duba yanayin tashe-tashen hankulan da ake fama da su a ƙasar. Kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito, Ningi ya ce bai kamata ƴan majalisar su kauda kai daga matsalar tsaron da ke damun wasu sassan ƙasar saboda su suna zaune a Abuja. “Mataki ne da ya zama…

Read More

Hon.Sha’aban ya jaddada janye neman takarar Sanatan Kaduna ta Arewa, tare da bayyana goyon duk wanda APC ta tsayar Cikin wata sanarwa da Iyalan Hon. Sani Sha’aban, Danburan Zazzau kuma Barden Keffi, suka fitar dauke da sanya hannun Alhaji Ahmad Bamalli ta bayyana cewar bisa wasu dalilai bayan shawarwarin da aka tattauna daga wannan rana ta Talata 21/4/2026 muna sanar da dukkannin magoya bayan Hon. Sani Sha’aban cewar ya janye daga neman takarar kujerar Sanata a Shiyyar Kaduna ta Arewa wato (zone one), tare da bayyana goyon baya ga duk dan takarar da APC ta tsayar. A cikin sanarwar an…

Read More

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya yi zargin cewa akwai wani sabon shiri na haɗa shi da aikata laifuka domin sake tsare shi. A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Muyiwa Adekeye, ya fitar, ya bayyana cewa wannan yunkuri na daga cikin wani tsari na ɓata masa suna da kuma hana shi samun ‘yanci. Sanarwar ta kuma ce El-Rufai na duba yiwuwar ɗaukar matakin shari’a kan jaridar The Nation, bisa wani rahoto da ta wallafa da ke danganta shi da wani hari da aka kai gidan wani shaida a Kaduna. Rahoton jaridar ya ambato…

Read More

Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Olufemi Oluyede ya buƙaci dakarun tsaron ƙasar su ƙara ƙaimi wajen yaƙi da ƴanbindiga a jihohin arewa maso yamma, inda ya nanata cewa dole a tabbatar Najeriya da ƴan Najeriya sun samu tsaro “ta kowane hali.” Janar Oluyede ya bayyana haka a ziyarar da ya kai wa sojojin da suke aiki na musamman na Fansan Yamma a garin Gusau da ke jihar Zamfara. Kotu ta bayar da sammacin kama tsohuwar ministan Buhari Sadiya Faruk bisa zargin badakalar kudade “Saƙona a fayyace yake: dole dakaru su fita su bi ɓatagari har maɓoyarsu su kawo ƙarshensu. Dole…

Read More

Babbar kotun tarayya da ke Abuja karkashin mai shari’a Jude Onwuegbuzie ta bayar da sammacin kama tsohuwar ministar harkokin jin kai, Sadiya Umar Farouq, da babban sakatare na ma’aikatar, Bashir Nura Alkali, bisa zargin karkatar da kudade. Hukumar EFCC na tuhumar su da laifuffuka 21 da suka hada da cin amanar aiki da karkatar da kimanin dala miliyan 1.3 da kuma sama da naira miliyan 746. ‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu Ana sa ran a gurfanar da su a kotu, amma ba su halarta ba, inda mutum na uku kawai, Sani Nafiu Mohammed, ya bayyana.…

Read More

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa da al’ummar Najeriya cewa gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen gina ƙasa mai dorewa, zaman lafiya, da wadata. Ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin da ya karɓi baƙuncin tawagar mambobin ƙungiyar Renewed Hope Ambassadors ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja. Shugaba Tinubu ya bayyana cewa tsarin siyasa da tattalin arziƙin da suka daɗe suna dakushe ci gaban ‘yan ƙasa, yanzu ana musanya su da sabbin tsare-tsare da za su ba kowa damar cin moriyar arziƙin ƙasa. Ya kuma…

Read More

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar, ya ce ba zai sake neman takarar shugaban ƙasar daga 2027 ba. Ya ce idan aka yi la’akari da shekarunsa da kuma damar da yake da ita ba lallai ya ci gaba da neman damar daga shekara mai zuwa ba. Atiku ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talabijin na Arise a ranar Laraba. Da aka tambaye shi game da cikarsa shekaru 80 a shekarar 2027 da yadda hakan zai iya daƙile masa damarsa, Atiku ya ce: “Tabbas za a samu ƙarin masu nema, kuma ita ce…

Read More