Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula da Hayar Gidaje A Kano 
Kano

Jam’iyyar Labour Party Ta Yi Alkawarin Kafa Hukumar Kula da Hayar Gidaje A Kano 

September 5, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
20260904 134856 COLLAGE

Ɗan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar Labour Party (LP), Alhaji Hamisu Santuraki, ya yi alkawarin kafa Hukumar Kula da Hayar Gida da ’Yan Hayar Gida, idan aka zaɓe shi a zaɓen 2027.

Santuraki ya ce manufar hukumar ita ce dakile ƙarin kuɗin haya ba bisa ƙa’ida ba da kuma kare ’yan haya daga cin zarafi da sauran matsalolin da suka shafi haya.

Ya bayyana hakan ne ta bakin mataimakinsa, Comrade Abbas Ibrahim, inda ya ce hukumar ba za ta sanya farashin haya iri ɗaya ga dukkan gidaje ba, sai dai ta tsara farashi bisa la’akari da wurin da gida yake, irin gidan, girmansa, yanayinsa da kayan more rayuwa.

Ya ce za a yi rajistar masu gidaje da kadarorin haya, sannan a ba dillalan gidaje lasisi tare da tsara kuɗin dillanci da sauran ka’idojin gudanar da sana’ar.

Santuraki ya ƙara da cewa hukumar za ta samar da tsarin kai ƙorafi da sasanta rikicin haya, musamman kan ƙarin haya ba bisa ƙa’ida ba, korar ’yan haya, tsadar kuɗin dillanci da cin zarafi.

A cewarsa, za kuma a samar da wani Rent Transparency Portal, wanda zai bai wa jama’a damar tantance gidaje, masu gidaje da dillalan da aka ba lasisi, da kuma sanin farashin hayar da aka amince da shi.

Ya ce za a rika bitar farashin haya lokaci zuwa lokaci bisa la’akari da hauhawar farashi, kuɗin gini, darajar gidaje da yanayin kasuwar haya.

“Manufar ba ita ce azabtar da masu gidaje ba, sai dai samar da kasuwar haya mai adalci, inda ’yan haya za su biya kuɗi na gari, yayin da masu gidaje su samu riba mai kyau,” in ji shi.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

AWOHI Ta Raba Kayan Tallafi A Gidan Kula Da Tsofaffi Na Shahuci Dake Kano

October 14, 2026

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 2026

Over 380 Arrested, 230 Convicted in Kano Drug Crackdown — Gov. Yusuf

October 1, 2026

Gwamnatin Kano Za Ta Tallafa Wa duk Wani Yunkurin Da Zai Kawar Da Ta’ammali Da Miyagun Ƙwayoyi A Jihar 

September 9, 2026

Kotu Ta Yanke Wa Mutane Biyu Daurin Shekaru 9 Kan Bai Wa Yara Kanana Kayan Shaye-shaye

September 8, 2026

Kano PHCMB Ta Nemi Haɗin Kan Al’umma Don Inganta Kiwon Lafiya

August 18, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Wakilan SNB Sun Shaida Tarihi Da Kyawawan Wuraren Yawon Buɗe Ido A Bauchi

October 2, 20267

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.