Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » CAF Ta Kwace Kofin AFCON 2025 Daga Senegal, Ta Bai Wa Morocco
Afrika

CAF Ta Kwace Kofin AFCON 2025 Daga Senegal, Ta Bai Wa Morocco

March 18, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
FB IMG 1773791354172

‎Hukumar ƙwallon ƙafa ta Afirka CAF ta kwace kofin zakarun nahiyar Afirka na 2025 daga ƙasar Senegal, tare da bai wa Morocco nasarar zama zakarun gasar.

‎Sanarwar da CAF ta fitar ta ce kwamitin sauraron ƙorafi na hukumar ya yanke hukuncin cewa tawagar Senegal ta karya dokokin gasar, bayan da wasu daga cikin ’yan wasanta suka fice daga filin wasa a yayin wasan ƙarshe domin nuna rashin amincewa da hukuncin alƙali.

‎Gamayyar Ƙungiyoyin APC sun amince da kungiyar Sen Yari The Renewed Hope Network TRN

‎Hukumar ta ƙara da cewa an ayyana Senegal da laifin watsi da wasa, wanda ya sa aka sauya sakamakon wasan daga 1-0 da Senegal ta samu zuwa 3-0 a hukumance domin Morocco.

‎Jaridar Inda Ranka  ta ruwaito cewa wasan ƙarshe na gasar ya gudana ne cikin yanayi mai cike da cece-kuce, musamman a ƙarshen lokaci inda aka bai wa Morocco bugun fenariti bayan duba VAR.

‎Hukuncin ya janyo fushin ’yan wasan Senegal, inda wasu suka dakatar da wasa na wani lokaci, lamarin da ya haifar da tsaiko na kusan mintuna 20.

‎A yayin rikicin, wasu daga cikin magoya bayan Senegal sun yi yunƙurin kutsawa cikin fili, tare da jefa wasu kayayyaki a cikin Filin, kafin jami’an tsaro su shawo kan lamarin.

‎A wasan dai, ɗan wasan Morocco Brahim Diaz ya kasa cin fenaritin, bayan mai tsaron ragar Senegal Edouard Mendy ya tare ƙwallon.

‎Daga baya ne kuma Pape Gueye ya ci ƙwallon da ta bai wa Senegal nasara a lokacin ƙarin lokaci, kafin hukuncin CAF ya soke sakamakon.

‎Hukuncin na CAF na ɗaya daga cikin matakan ladabtarwa da ke haifar da muhawara, musamman duba da yadda wasan ƙarshe ya kasance mai cike da rikice-rikice.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.