Har yanzu babu ƙasa ko guda 1 da ta amsa buƙatar Donald Trump wajen aika jirgi mashigin Hormuz cikin ƙasashe 5 da shugaban na Amurka ya nemi su aike da jiragen yaƙinsu na ruwa tare da sojojinsu don yiwa jiragen dakon mai rakiya a mashigin na Hormuz da Iran ta kulle.
A jiya Asabar ne Trump ya nemi ƙasashen China da Faransa da Japan da Korea ta kudu da kuma Birtaniya kan su aike da jiragen yaƙi zuwa mashigin na Hormuz don ƙalubalantar shingen da Iran ta sanya wanda ya hana safarar makamashi.
Gwamnatin Najeriya ta ɓullo da shirin samar da tsayyayiyar wutar sola a asibitoci 371
Japan ce ƙasa ta farko da ta fara mayar da martani kan kiran na Trump inda ta ce babu yadda za a yi su tashi jirgin yaƙi zuwa mashigin na Hormuz kawai don Trump ya buƙaci haka.
A gefe guda Birtaniya ta bakin ministan tsaron ta ya shaidawa wata kafar labarai ta Amurka cewa, ƙasar yanzu haka na tattaunawa da ƙawayenta don laluben hanyoyin da za a dawo da hada-hadar makamashi a yankin na gabas ta tsakiya.
China wadda ke matsayin ƙawa ga Iran ta nanata cewa za ta so ɓangarorin da ke yaƙar juna su kawo ƙarshen shigar da ƴan baruwanmu cikin rikicin yayinda ta yi fatan dawowar hada-hadar makamashi don amfanin jama’a.
Faransa cikin wani saƙo da ministan harkokin wajen ƙasar ya wallafa a shafin X ya ce ƙasar ba zata aika da jiragen yaƙi mashigin na Hormuz ba, haka zalika babu wani jirgin yaƙin Faransa na ruwa ko na sama da za a ga gilmawarsa ko kuma zuwansu gabashin tekun na Mediterranean.
Sai dai an jiyo shugaban Korea ta kudu na cewa suna nazartar buƙatar ta Trump kuma suna tattaunawa da Amurka kan batun.
Kafin yanzu dai wata sanarwar ma’aikatar tsaro da ta kasuwanci a Amurkan sun bayyana cewa ƙasar ba zata yi kasadar tura dakarun Sojin ruwa kawai don baiwa jiragen dakon makamashi kariya a mashigin na Hormuz ba.
Akwai fargabar cewa Iran ta dasa ababen fashewa a mashigin na Hormuz.

