Hukumar Shari’ah ta Jihar Jigawa (JSC) ta amince da tilasta wa alƙalin Kotun Shari’ar Musulunci da ke jihar yin ritaya. Wannan na ƙunshe ne a wata takarda babban jami’in yaɗa labaran JSC, Abba Wangara ya fitar a yau Talata, a Dutse. BINCIKE: An samu karin kashi 543% a yaduwar cutar dajin dake kama nono a Najeriya Haka kuma, hukumar ta amince da ƙarin matsayi ga wasu jami’anta guda 80 a muƙamai daban-daban. Ya bayyana cewa, an ɗauki matakin ne yayin wani zama da hukuncin ta gudanar a Dutse. A cewarsa, bayan bincike mai zurfi da samar da hujja mai ƙarfi…
Author: Wafsym
Sakamakon binciken da ‘Global Burden of Disease’ ta gudanar ya nuna cewa Afrika na daga cikin barayin duniya dake samun karuwa a yaduwar cutar dajin dake kama nono inda kasar Equatorial Guinea ta samu karin kashi 312% karin da ya fara daga shekarar 1990 har zuwa yanzu. An wallafa wannan sakamakon a ‘Lancet’ ranar Litini sannan an gudanar da binciken ta hanyar tantance takardun dake dauke da yawan mutanen dake fama da cutar da tattaunawa da masu fama da cutar, iyalen sun da jami’an lafiyan dake Kula da masu fama da cutar. Kashi 30% Ne Kwai Na Yaran Daya…
Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen sabinta rijartar mambobinsu yayin da wa’adin da aka gindaya domin kowacce ta miƙawa hukumar zaɓen ƙasar cikakkiyar rijistar ke kawo jiki. Wannan na daga cikin shirye-shiryen tunkarar baban zaɓen ƙasar na 2027. A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam’iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026. Umarnin da INEC ta bai wa jam’iyyun siyasar na daga cikin tanadin dokar zaɓen Najeriya ta 2026, wadda ke neman inganta yadda jam’iyyun siyasar ƙasar ke gudanar da harkokin…
Babban Sakataren Hukumar Bunkasa Harkokin Ilimi ta Kasa, Farfesa Salisu Shehu, ya ce kashi 30 cikin 100 kacal na yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta ke zuwa Arewacin Najeriya. Ya bayyana hakan ne a yayin taron Ramadan karo na 10 da Islamic Forum of Nigeria ta shirya a Kano. Jami’ar Osun Ta Buƙaci Wani Kamfani Ya Janye Kalamansa Kan Batun Ma’aikatan Bogi A Jami’ar Farfesan ya ce sama da yara miliyan 20 ne a Najeriya ba sa zuwa makaranta, yana mai danganta hakan da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da kuma…
Shugabannin jami’ar Jihar Osun (UNIOSUN) sun yi kira da suna kamfanin Sally Tibbot Ltd cewar ya rubuta takardar neman a yafe mata a kan rahoton binciken yadda aka biya albashi inda har aka gano da ‘’akwai ma’aikatan Bogi da suka kai 250 .” Da yake ganawa da manema labarai ranar Asabar, a Osogbo, mataimakin Shugaban jami’ar Farfesa.Clement Adebooye, ya yi barazanar cewar Jami’ar na iya ɗaukar matakin shari’a domin tana son abi mata ba’asin da ya kai ga sa yi mata irin wannan cin fuskar, matuƙar shi kamfanin yaƙi lashe aman da ya yi na zarginsu da hakan ba cewar…
Ƴanta’adda sun kashe mayakan sa-kai akalla 25 yayin wani harin da suka kai ƙauyuka hudu na jihar Tillabery da ke yammacin jamhuriya Nijar. Majiyoyi sun sun ce ƴanta’addan sun kai harin ne ranar 26 ga watan Fabarairu 2026 a yankin Anzourou da ke kan iyaka kasar da Mali. Iran Ta Tabbatar Da Kisan Ali Khamenei Da Iyalansa Dakarun sa-kan na aikin tabbatar da tsaro a kauyukansu ne lokacin da ƴanta’addan suka far musu. Wanan harin na zuwa a daidai lokacin da mayaka masu ikirarin jihadi ke cigaba da kwarara a yankin da matsalar tsaro ta yiwa illa. A makwonni uku…
Kafar watsa labaran gwamnatin Iran ta ce an kashe Jagoran Addinin ƙasar Ayatollah Ali Khamenei a harin da Isra’ila da Amurka suka kai, lamarin da ya sanya kiraye-kiraye ga rundunar juyin-juya-hali ta Revolutionary Guards domin ta ɗauki matakin ramuwar gayya. Gidan talbijin na ƙasar Iran ranar Lahadi ya sanar da makokin kwana 40 tare da bayar da hutun kwana bakwai bayan kisan shugaban addinin ƙasar mai shekara 86, wanda ke kan mulki tun shekarar 1989. Kafofin watsa labaran Iran sun ruwaito cewa a kashe ‘yar Ayatollah Ali Khamenei da jikarsa da kuma surukinsa a harin. “Shahadar da shugaban addini ya…
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanar da dakatar da wasan gargajiya na Tashe a duk faɗin jihar a wannan watan na Ramadan, saboda dalilan tsaro. Hukumar ta ce an ɗauki matakin ne tare da haɗin gwiwar gwamnatin jihar domin hana masu aikata laifi amfani da tarukan Tashe wajen aikata miyagun ayyuka, ciki har da daba, ƙwacen waya da kuma shaye-shayen miyagun ƙwayoyi. Tinubu ya sake naɗa Abubakar Audi a Kwamanda Janar Na NSCDC Kwamishinan ’yan sandan jihar, Ibrahim Adamu Bakori, ya bayyana cewa rundunar ta tanadi matakan tsaro domin tabbatar da an gudanar da azumin cikin zaman lafiya da…
Shugaba Bola Tinubu ya sake naɗa Dakta Ahmed Abubakar Audi a matsayin Kwamanda-Janar na Hukumar Tsaron al’umma ta Cibil Defense (NSCDC) na wani sabon wa’adin shekaru biyar. Sabon naɗin ya fara aiki ne q ranar Juma’a, 27 ga Fabrairu, 2026 . Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a —Rahoto na musamman An fara naɗa Dakta Audi a wannan matsayi ne a shekarar 2021 ta hannun tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Wa’adinsa na farko na shekaru biyar ya ƙare ne a ranar Juma’ar da ta gabata yayin da…
Daga Salisu Ibrahim Fagge tare da haɗin gwiwar Abbas Ibrahim, Mohammed Kabir Yau, Abdullahi Yusuf, Mustapha Muhammad da Kabiru Fulatan Kasuwancin dabbobi a Kano na kara bunƙasa cikin sauri, yayin da buƙatar nama, madara da fata ke ƙaruwa a sassan Najeriya. Amma duk da wannan ci gaba, wani bincike na musamman ya nuna cewa ana fuskantar babbar barazana ta ɓoye sakamakon yawaitar amfani da wani sinadarin magani da ake yiwa lak’abi da (kira) “Sha Ka Fashe.” Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita Binciken ya gano cewa wasu…
