Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Yadda Jam’iyyar APC Da ADC Ke Sabinta Rigistar Mambobinsu
Siyasa

Yadda Jam’iyyar APC Da ADC Ke Sabinta Rigistar Mambobinsu

March 3, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
b7eb0670 16b9 11f1 801d ed3cff6bf876.jpg

Jam’iyyun siyasa a Najeriya sun ƙara ƙaimi wajen sabinta rijartar mambobinsu yayin da wa’adin da aka gindaya domin kowacce ta miƙawa hukumar zaɓen ƙasar cikakkiyar rijistar ke kawo jiki.

Wannan na daga cikin shirye-shiryen tunkarar baban zaɓen ƙasar na 2027.

A ƙarƙashin sabon jaddawalin zaɓen da hukumar zaɓen Najeriya, INEC ta fitar, ana buƙatar jam’iyyun siyasar ƙasar su gabatar da cikakkiyar rijistar mambobinsu ya zuwa ranar 2 ga watan Afirelun 2026.

Umarnin da INEC ta bai wa jam’iyyun siyasar na daga cikin tanadin dokar zaɓen Najeriya ta 2026, wadda ke neman inganta yadda jam’iyyun siyasar ƙasar ke gudanar da harkokin su na cikin gida da kuma samar da tsari mai kyau na fitar da ƴan takara a cikin jam’iyyun.

Wannan na zuwa ne yayin da wasu masu sharhi ke gnin cewa jam’iyyun na da ƙarancin kayan aiki na cika ƙa’idar hukumar zaɓe (INEC) wadda ke neman rijistar mambobin jam’iyyun siyasar ya zamo ta hanyar amfani da fasahar zamani, musamman ta la’akari da ƙurarren lokacin da aka ware domin wannan aiki.

Jam’iyyar APC mai mulkin ƙasar ta ce ta fara aikin sabinta rijistar mambobin nata, wanda ta ce yaa gudana cikin nasara a dukkan mazaɓun ƙasar ciki harda na Abuja babban birnin Najeriya.

Sanarwar da sakataren yaɗa labaran jam’iyyar Felix Moka ya wallafa a shafinta na X, ta ce aikin zai samar da cikakkiyar rijistar mambobin APC na ƙasar, ya kuma tabbata jam’iyyar ta cika ƙa’idar shiga zaɓe mai zuwa.

Ya yi bayanin cewa tsaffin ƴaƴan APC da kuma sabbi ne suka yi wannan rijista ta amfani da lambar katinsu na ƴan ƙasa wato NIN.

APC ta ce wannan dama ce ga dukkan ƴan Najeriya da suka cika shekara 18 su shiga dama ta shiga a dama da su a fagen siyasar ƙasar, musamman a wannan lokaci da jam’iyyar ta ce tana aiwatar da sabon tsarin bunƙasa fahimtar juna tsakanin mambbinta.

Itama jam’iyyar adawa ta ADC ta soma rajistar inda a cikin wani bayani da ta fitar mai dauke da sa hannu sakataren watsa labaranta na ƙasa Bola Abdullahi, ta bayyana cewa ta fara aikin mambobinta ta hanyar latironi domin tunkarar manyan zabukan 2027 da ma na share fage a nan gaba kadan.

Jam’iyyar ta ce a yanzu haka dubban ‘ya’yanta a fadin Najeriya na ci gaba da yin rajistar.

Jam’iyyar ta ADC da ke gaba-gaba a jam’iyyun adawar kasar ta bayyana cewa sai wadanda suka yi cikakkiyar rajista da ita kuma aka dauki bayanansu ne za su shiga zabukanta na share fage.

Faisal Kabir shi ne mai magana da yawun jam’iyyar ta ADC a Najeriya kuma ya shaidawa BBC cewa ”Babu abin da za mu ce sai godiya, yadda ƴan Najeriya suka fito suka nuna cewa suna tare da ADC, domin ni jiya na yi tunanin ma dukkan ƴan Najeriya ne suke jam’iyyar ADC.”

Ya ce rijistar ta su ta bayar da mamaki, kuma ta zarce wadda jam’iyyar APC mai mulki ke yi.

”Kowa zai je mazaɓar shi ya yi rijista, kuma muna yin shi online yadda kowa zai iya ɗaukar wayar hannunsa ya yi cikin kwanciyar hankali.”

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

March 6, 2026

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita

February 27, 2026

Shugaba Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

February 23, 2026

Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami

February 21, 2026

Rundunar ‘yan sandan Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga a kananan hukumomin birnin kano da Ungogo

February 21, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.