Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Kashi ‎ 30% Ne Kwai Na Yaran Daya Kamata Suje Makaranta Suke Zuwa A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Farfesa Shehu
Afrika

Kashi ‎ 30% Ne Kwai Na Yaran Daya Kamata Suje Makaranta Suke Zuwa A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Farfesa Shehu

March 3, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260302 204513 741

Babban Sakataren Hukumar Bunkasa Harkokin Ilimi ta Kasa, Farfesa Salisu Shehu, ya ce kashi 30 cikin 100 kacal na yaran da suka kai shekarun zuwa makaranta ke zuwa  Arewacin Najeriya.

‎Ya bayyana hakan ne a yayin taron Ramadan karo na 10 da Islamic Forum of Nigeria ta shirya a Kano.

‎Jami’ar Osun Ta Buƙaci Wani Kamfani Ya Janye Kalamansa Kan Batun Ma’aikatan Bogi A Jami’ar

‎Farfesan ya ce sama da yara miliyan 20 ne a Najeriya ba sa zuwa makaranta, yana mai danganta hakan da matsalolin tsaro da suka hada da hare-haren ’yan bindiga a Arewa maso Yamma da kuma rikicin tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas, lamarin da ya haddasa rufe makarantu a wasu jihohi.

‎Ya kuma nuna damuwa kan karancin malamai sakamakon ritaya, sauyin aiki da rasuwa, yana mai gargadin cewa rashin ilimi na kara haddasa rashin zaman lafiya da ta’addanci.

‎Farfesa Shehu ya bukaci gwamnonin Arewa su ayyana dokar ta-baci a bangaren ilimi, su kuma kara zuba jari domin farfado da tsarin koyarwa. Ya ce kasashe kamar Bangladesh da Malaysia sun taba fuskantar irin wannan kalubale, amma suka samu ci gaba ta hanyar hadin gwiwar gwamnati da al’umma.

‎Ya kuma soki abin da ya kira fifita wasu abubuwa marasa muhimmanci a kan ilimi, yana mai cewa ya kamata a ba ilimi fifiko domin ceto makomar matasa.

‎A nasa jawabin, Alhaji Ibrahim Ado Kurawa ya danganta tabarbarewar tsaro da sauyin yanayi da rikicin manoma da makiyaya, yana mai cewa hakan na kara jefa yankunan Arewa cikin talauci da fatara.

‎Shi kuma Farfesa Kabiru Isa Dandago ya ce talauci, rashin aikin yi da tsadar rayuwa na daga cikin manyan kalubalen da ke barazana ga ci gaban yankin.

‎Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa, Malam Ibrahim Khalil, ya jaddada muhimmancin shugabanci mai gaskiya da kishin kasa, yana mai cewa hakan ne mafita ga kalubalen da Arewacin Najeriya ke fuskanta.

‎Taron ya kuma samu halartar manyan baki da dama, ciki har da Sarkin Rano, Amb. Muhammad Isa Umaru.

‎

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.