Hukumar ICPC mai yaƙi da cin hanci da rashawa a Nijeriya ta ƙaddamar da mataki na takwas na shirin bibiyar ayyukan mazaɓu da na sashen zartarwa a Jihar Katsina, inda ake sa ido kan jimillar ayyuka 39 da kuɗin su ya kai naira biliyan 13.5 a yankunan sanatoci da mazaɓun tarayya na jihar. A cewar hukumar, tawagar bibiyar ayyukan ta haɗa da manyan jami’ai daga hedikwata da ofishin Katsina. Kotu Ta Ci Tarar Ƴansanda Naira Miliyan 30 Kan Ayyana Neman Sowore Ruwa A Jallo Hukumar ta ce ana gudanar da aikin ne tare da haɗin gwiwar Nigerian Institute of Quantity…
Author: Wafsym
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta yanke hukunci cewa Rundunar ‘Yansandan Nijeriya, ta aikata kuskure da ya saɓa ƙa’ida na ayyana ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan Adam kuma mawallafin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo a shekarar 2025. Yayin yanke hukunci a ranar Juma’a, Mai shari’a Musa Kakaaki, ya bayyana cewa matakin da ’yansanda suka ɗauka ya saɓa wa tanade-tanaden kundin tsarin mulki tare da nuna amfani da iko da bai dace ba, inda ya jaddada cewa babu wanda ya zama mai laifi saboda amfani da ’yancin faɗar albarkacin bakinsa ko gudanar…
A ƴan kwanakin baya-bayan nan an yi ta muhawara musamman a kafofin sada zumunta kan batun siyasar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Farfesa Ali Isa Pantami. A farkon watan Fabarairu ne tsohon ministan sadarwar na Najeriya ya sake motsa siyasarsa bayan ya je harabar sakatariyar jam’iyyar APC a jihar Gombe inda ya sabunta rajistarsa. Sheikh Pantami ya kuma zagaya sassan birnin Gombe bisa rakiyar dubban magoya bayansa a wani mataki na nuna neman goyon bayan jama’a. Duk da kasancewar Farfesa Pantami tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, da dama ƴan ƙasar ba sa yi…
Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta sanya dokar takaita zirga-zirga a ƙananan hukumomin birnin kano da Ungogo na tsawon awanni 18, gabanin zaɓen cike-gurbi na ‘yan majalisar dokokin jihar kano da za a gudanar a yau Asabar. ’Yan sandan sun ce dokar, wadda za ta fara aiki daga ƙarfe 12:00 na dare zuwa ƙarfe 6:00 na yamma a ranar Asabar, ta shafi motocin haya da masu zaman kansu, babura masu ƙafa uku da kuma babura masu kafa biyu, a matsayin wani mataki na inganta tsaro domin tabbatar da an gudanar da zaɓe cikin kwanciyar hankali. Jihohin Najeriya da suka fi…
Yayin da aka shiga wata na biyu a shekarar 2026, tuni gwamnonin jihohin Najeriya suka fara gudanar da wasu daga cikin ayyukan da suka tsara cikin kasafin kuɗin shekarar. A wanann shekarar jihohin sun ƙara kuɗaɗe masu yawa cikin kasafinsu na shekarar da muke ciki, wani abu da ke nuna yadda jihohin ke samun ƙarin kuɗaɗe daga tarayya. Shugaba Tinubu ya naɗa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban kwamitin ciyarwar Ramadan na Ƙasa Jihohi da dama sun kafa hujja da burin gudanar da manyan ayyukan ci gaba wajen ƙara yawan kuɗaɗen da za su kashen a 2026. Haka…
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya naɗa Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, a matsayin Shugaban Kwamitin Ciyarwar Azumin Ramadan na Ƙasa. Wannan shiri na gwamnatin tarayya zai kula da rabon kayan abinci kamar shinkafa, gero da mai ga al’umma a duk faɗin Najeriya, domin rage raɗaɗin rayuwa a wannan wata mai alfarma. Da Dumi Dumi An ga watan Azumi a Nijeriya Sarkin ya yaba da wannan mataki, yana mai cewa shiri ne mai muhimmanci, tare da alƙawarin bada cikakken goyon baya domin nasarar sa.
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya ICPC ta sanar cewa tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasiru El-Rufai, na hannunta daga jiya ranar Laraba 18 ga Fabrairu 2026. Sanarwar wadda mai magana da yawun hukumar, J. Okor Odey, ya fitar ta ce “El-Rufai na hannun mu a halin yanzu domin tambayoyi masu alaƙa da bincike, kuma yana cikin kulawar hukumar a halin yanzu.” Da Dumi Dumi An ga watan Azumi a Nijeriya Hakan na zuwa ne bayan da tsohon gwamnan ya shafe kwanaki biyu a hannun EFCC, inda ya kai kansa ranar Litinin domin amsa gayyata kafin daga bisani…
Fadar Sarkin Musulmi ta bayyana cewa an ga jinjirin watan Azumin Ramadan a na shekarar Musulunci ta 1447, a Najeriya. Cikin wata sanarwa da fatar Sarkin Musulumin ya fitar a ranar Talata da daddare, ya ce an samu bayanan ganin watan a wurare daban-daban a ƙasa. Tsarin Siyasar Kano : Ya Kamata Gwamna Abba Ya Yunkura Kafar BBC Hausa ta ruwaito cewa, fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ta umarci Musulman Najeriya, su fara azumin Watan Ramadan a ranar Laraba 18 ga watan Fabrairun 2026. Matakin na alamta shigar watan Ramadan mai alfarma – wanda musulmi a faɗin duniya ke gudnar…
Daga Abba Anwar A bayyana ne yake, abinda ya faru jiya a wurin taron bikin karbar Gwamna Kano Abba Kabir Yusuf zuwa cikin jam’iyyar APC wanda aka gudanar a filin wasa na Sani Abacha, wanda ya samu halartar Mataimakin Shugaban Kàsa Kashim Shettima, GCON, wani ma’auni ne da yake haska wanda ya fi shiri kan zaben shekara ta 2027 tsakanin Gwamna da jagororin APC a jihar Kano. Tashin farko idan mutum ya yi nazarin taron zai fahimci cewa da yawa daga cikin wadanda su ka jagoranci shirya taron a bangaren Gwamna, ko dai sun nuna sakaci da lalaci, ko su…
Hukumar tsaron farin kaya a Najeriya ta shigar da tuhuma guda uku kan tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufai, bisa zargin shi da hannu bisa naɗar wayar mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan tsaro Malam Nuhu Ribadu. A ƙarar da ta shigar mai lamba FHC/ABJ/CR/99/20262003 a safiyar yau Litinin a babbar kotun tarayya da ke babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, DSS ta tuhumi tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i da amincewa da aikata datsar wayar mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan tsaro. Fiye da Kananan Yara Miliyan Biyu Ke Gararamba A Titunan Kano — NGO Takaddar…
