Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami
Labaran Duniya

Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami

February 21, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
62e17350 0e79 11f1 801d ed3cff6bf876.png

A ƴan kwanakin baya-bayan nan an yi ta muhawara musamman a kafofin sada zumunta kan batun siyasar fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Najeriya, Farfesa Ali Isa Pantami.

A farkon watan Fabarairu ne tsohon ministan sadarwar na Najeriya ya sake motsa siyasarsa bayan ya je harabar sakatariyar jam’iyyar APC a jihar Gombe inda ya sabunta rajistarsa.

Sheikh Pantami ya kuma zagaya sassan birnin Gombe bisa rakiyar dubban magoya bayansa a wani mataki na nuna neman goyon bayan jama’a.

Duk da kasancewar Farfesa Pantami tsohon minista a gwamnatin tsohon shugaban Najeriya, Marigayi Muhammadu Buhari, da dama ƴan ƙasar ba sa yi masa kallon ɗan siyasa, a maimakon haka suna ganin Buhari ya naɗa shi muƙamin ne sanadiyyar ƙwarewarsa a fannin fasahar sadarwa.

Ana dai alaƙanta fitaccen malamin addinin da tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya.

BBC ta tattauna da fitaccen malamin – wanda a baya ya sha sukar tsarin siyasar Najeriya – ya bayyana dalilansa na shiga siyasa gadan-gadan.

Sheikh Pantami ya ce ya jima da shiga siyasa, kuma a matsayinsa na dan Najeriya kundin tsarin mulkin ƙasar ya ba shi damar shiga harkokin siyasar ƙasar.

”Da farko ma kundin tsarin mulkin Najeriya ya yi tanadin cewa ba za ka taba zama minista a ƙasar nan ba sai kana da katin jam’iyya”, in ji malamin.

Don haka malamin ya ce a yanzu duk wanda yake riƙe da muƙamin minista, in dai ba shi da katin jam’iyya to ya saɓa wa doka.

Sheikh Pantami ya ce ya fara yankar katin jam’iyyar ne bayan da Buhari ya sanar da sunansa cikin ƙunshin ministocin gwamnatinsa a watan Yulin 2019.

”Na kuma yi hakan ne domin na cika ƙa’idar zama ministan da aka bukace ni, tun da ba ni na nema ba”, in ji malamin addinin.

Amma Farfesa Pantami ya ce tun kafin lokacin yankar katin nasa yana shiga harkokin siyasa.

”Abin da ake nufi da siyasa fa shi ne shugabanci nagari, don haka duk mutum mai nagarta na da sha’awar samar da shugabanci nagari”, in ji shi.

Fiye da shekara 20 muna kira ga mutane su shiga harkar samar da shugabanci nagari, mu ne dai akwai lokacin da ba mu shiga , akwai kuma lokacin da muka shiga.

‘Abin da ya kaini ofishin APC a Gombe’

Sheikha Pantami ya ce abin da ya kai shi ofishin APC na jihar Gombe shi ne sabunta rajistarsa.

”Ba wai na je domin yankar katin jam’iyya ba ne, dama ina da kati, na je ne domin sabunta rajistata”, kamar yadda ya bayyana cikin hirarsa da BBC.

Fitaccen malamin ya ce ya fara yankar katin jam’iyyar ne shekaru takwas da suka gabata lokacin da aka naɗa shi minista.

‘Ban taɓa haramta shiga siyasa ba’

A baya dai an sha jin malamin na sukar tsarin siyasar Najeriya, sai ya ce ya kasance mai rajin shugabanci nagari.

”Ban taɓa cewa shiga siyasa haramun ba ne, idan akwai wanda ya taɓa ji , ina so ya kawo min wurin,” in ji shi.

Sheikh Pantami ya ce galibin bidiyoyinsa na baya da a yanzu suke yawo a shafukan sada zumunta an jirkita su ne.

”Galibin waɗannan bidiyoyin an yayyanke su an jojjona su da juna, galibi ba a kan maudu’in da ake magana na yi su ba,” in ji shi.

”Don haka ni ban taba haramta shiga siyasa ba,” in ji Sheikh Pantami.

‘Wajibi ne mutane masu nagarta su shiga siyasa’

Sheikh Pantami ya ce ya sha jin manyan malamai masu nagarta a ciki da wajen Najeriya da ma manyan magabata na kiran mutane masu nagarta su shiga siyasa.

”Ina da sautin Sheikh Abubakar Mahmud Gumi, da Sheikh Dahiru Bauchi da Dr Bashir Aliyu Umar da Dr Sani Umar Rijiyar Lemo da wasu da dama na kiran cewa ya kamata mutane masu nagarta su shiga siyasa,” in ji shi.

Fitaccen malamin addinin ya kuma ce yana da fatawoyin manyan malaman duniya da suka ce a shiga siyasa.

”Akwai fatawar Ibn Usaymin da yake cewa shigar siyasa ga mutane masu nagarta wajibi ne, Dokta Bashir cewa ya yi shigar mutane masu daraja wajibi ne,’’ in ji Pantami.

Wasu dai na sukar shigar malamai siyasa da cewa hakan zai zubar da kimarsu, to amma Sheikh Pantami ya ce duk wanda yake wannan tunani to akwai rashin ilimi ko son rai.

”Ai ba yau masu addini suka fara shiga siyasa ba, an samu wasu manyan malamai a Kano da Neja da suka tsaya takara,” in ji shi.

‘Abin da ya sa zan tsaya takarar gwamnan Gombe’

Dangane da hasashen da wasu ke yi cewa malamin na sha’awar tsayawa takarar gwamnan jihar Gombe, ya ce ba shi ya fara sha’awar batun ba.

”Akwai ƴan’uwa da dama waɗanda tun da na bar ofishin ministan sadarwa, bayan ganin ɗimbin ayyukan alkairan da na kai wa jihar Gombe na sama wa yara ayyukan yi da horas da mata da bayar da tallafi da sauransu”.

‘’Su ne suka ga dacewar tsayawata takarar gwamnan jihar Gombe, inda suka riƙa tururuwar na zo na shiga na tsaya takarar gwamnan,” a cewarsa.

Malamin ya ce da fari ya nuna yana ƙin abin, amma daga baya bisa shawarar abokansa da neman zaɓin Allah ya ji ya gamsu zai iya tsayawa.

”Har istikara a ɗakin ka’aba sai da na yi domin neman zaɓin Allah, sai na ji ƙiyayyar da nake yi wa takarar tana raguwa, har daga baya na zo na ji na gamsu,” in ji tsohon ministan sadarwar.

‘Abin da zan mayar da hankali in na zama gwamnan Gombe’

Sheikh Pantami ya ce ya ce idan har Allah ya huwace masa ya zama gwamnan Gombe zai ɗora kan ayyukan da gwamna jihar na yanzu ke yi wa jihar.

”Babban abin da za mu mayar da hankali a kai shi ne samar da ayyukan gina al’umma da kafa masana’antu, janyo masu zuba jari daga ƙetare.”

Malamin ya ce zai kuma bunƙasa tattalin arziki ta hanyar samar wa matasa da mata ayyukan yi, ta hanyar samar musu sana’o’i da ilimin zamani.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamnan Kano ya sauke shugaban ma’aikatan jihar Alhaji Abdullahi Musa daga mukaminsa

March 11, 2026

Sojojin UAE biyu sun mutu a hatsarin jirgin sama – Ma’aikatar tsaro

March 10, 2026

Mojtaba Khamenei Ya Gaji Mahaifinsa A Matsayin Jagoran Addinin Iran

March 9, 2026

Farashin litar man fetur ya zarce naira dubu 1 a sassan Najeriya

March 9, 2026

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Yakin Amurka/Isra’ila da Iran: Lallai da ni za a zaɓi sabon shugaba a Iran – Trump

March 6, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.