Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ana ci gaba da matsa wa DSS lamba kan ta saki Walida
Afrika

Ana ci gaba da matsa wa DSS lamba kan ta saki Walida

February 24, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
f69eabf6 97ec 4014 97cc 2f385974e3a2.jpg

Wani lauya mai rajin kare haƙƙin bil’adama a Najeriya, Barista Hamza Nuhu Dantani ya rubuta wata wasiƙa zuwa ga Hukumar tsaron farin kaya DSS ta ƙasar, inda yake nuna damuwa dangane da yadda ya ce hukumar ta ɗauki batun zargin sacewa, da kuma yin lalata da wata mace, Walida Abdulhadi, da ake zargin ɗaya daga cikin jami’anta Ifeanyi Onyewuenyi da yi.

A cikin wasiƙar, lauyan ya saka ayar tambayar kan dalilan ƙin miƙa yarinyar ga iyayenta da kuma abin da ya kira ƙoƙarin kare jami’in da hukumar ke yi.

Ƴan Bindiga sun sa harajin miliyan 100 ga malaman da ke son yin wa’azi a Kebbi

Batun matashiyar na ci gaba da ɗaukar hankali a Najeriya tun bayan da wasu gungun lauyoyi suka shigar da ƙara suna zargin wani jam’in hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya (DSS) da laifin “sacewa da yin lalata da kuma sauya wa wata yarinya mai suna Walida Abdulhadi addini.”

 

Rahotanni sun bayyana cewa jami’in na hukumar DSS ne ya tuntuɓi iyayen yarinyar, inda ya shaida musu cewa yana riƙe da ita, kuma har ta haifa masa ɗa, a wata unguwa da ke Abuja, babban birnin Najeriya.

 

A cikin koken da Barista Nuhu ya rubuta, ya ce “An ɗauke yarinyar ne a lokacin da take aji biyu a babbar sakandare, kuma mahaifinta ya sha nanata cewa ƙaramar yarinya ce a lokacin da ta ɓace.”

 

Lauyan ya buƙaci a miƙa ta zuwa ga iyayenta, inda ya ƙara da cewa babu dokar da ta ba DSS damar ci gaba da riƙe matashiyar. “Don haka ina kira da a saki Walida ba tare da ɓata lokaci ba, sannan wasu daban su gudanar da bincken ba DSS ba.”

Haka kuma wasu ƙungiyoyin rajin kare haƙƙin ɗan’adam sun kai nasu koken, inda suka buƙaci DSS ta gaggauta sakin Walida, domin a cewarsu tana ƴar shekara 16 ne ya tafi da ita.

Ƙungiyoyin, waɗanda suka rubuta koken a ƙarƙashin Gamji Lawchain a madadin mahaifin yarinyar, sun yi zargin cewa jam’in ya sace ta, sannan ya yi lalata da ita, tare da tilasta mata komawa addinin Kirista.

Daga cikin ƙungiyoyin akwai International Human Rights Commission Relief Fund Trust (IHRC-RFT) da Women Voices and Accountability da Muslim Rights Concern (MURIC) da sauransu.

 

BBC

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.