Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da fuskantar yunƙurin juyin mulki ga gwamnatin ƙasar a kwanakin baya, wanda ta ce ta gano hakan ne bayan tsananta bincike kan wasu jami’anta da ta zarga da rashin ɗa’a inda sakamako ya tabbatar da cewa tabbas sun yi shirin kifar da gwamnatin ƙasar. Tun a watan Oktoban 2025 ne, shalkwatar tsaron Najeriyar ta sanar da kame wasu manyan sojoji 16 bayan zarginsu da saɓa dokokin aiki, kodayake a wancan lokaci ta ƙi amsa zargin cewa sun yi shirin kifar da gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu ne. Ƙungiyar SERAP Ta Maka Ministan Wutar Lantarki Da…
Author: Wafsym
Ƙungiyar kare haƙƙin jama’a da sa ido kan kashe kuɗaɗen gwamnati, a Najeriya, SERAP ta shigar da ƙara a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan Ministan Wutar Lantarki, Adebayo Adelabu, da Hukumar Kula da Lantarki ta Najeriya NBET, bisa zargin karkatar da Naira biliyan 128. SERAP ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bayan zarge-zargen da ke cikin rahoton Babban Mai Binciken Kuɗi na Tarayya da aka wallafa a watan Satumba na bara. “Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai —Comrade Abbas Ibrahim Ƙungiyar na neman kotu…
Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta sanar cewa rajistar UTME 2026 za ta fara ne daga Litinin, 26 ga Janairu, zuwa 28 ga Fabrairu, a dukkan cibiyoyin kwamfuta (CBT) da hukumar ta amince da su a fadin Najeriya. Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka ne a Legas yayin taro da Kwamishinonin Ilimi na jihohi. Ya ce sayar da takardar neman rajista (e-PIN) zai fara daga 19 ga Janairu kafin fara rajistar kai tsaye. “Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai —Comrade Abbas…
Tsohon Shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida ta Ƙasa (NUJ), reshen jihar Kano, Comrade Abbas Ibrahim, ya jaddada muhimmancin gudanar da aikin jarida cikin tausayawa da hikima, musamman wajen ɗauko labarai da suka shafi masifu, raɗaɗi ko wahalhalun rayuwar mutane. A cewarsa, aikin jarida ba wai tattara bayanai kawai ba ne, har da la’akari da halin da mutumin da abin ya shafa yake ciki. Tsadar Data Ta Jefa Ɗaliban Karatu Daga Nesa Cikin Ƙunci A Najeriya “Ya kamata a dubi yanayin mutum kafin a fara yi masa tambayoyi, musamman idan yana cikin damuwa ko rashin lafiya,” in ji Abbas…
Ƙaruwar farashin sayen damar shiga shafukan Intanet, wato data, na ci gaba da jefa ɗaliban da ke dogaro da karatu daga nesa cikin mawuyacin hali, inda da dama ke korafin cewa hakan na kawo musu cikas wajen ci gaba da neman ilimi. Wasu ɗaliban da wakilinmu ya zanta da su sun bayyana cewa tsadar data na hana su halartar darussan Intanet yadda ya kamata, tare da rage musu damar yin bincike, sauke littattafai da kuma shiga ajujuwan koyarwa ta yanar gizo. Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa Ya Yi Allah-wadai Da Kashe Matar Aure Da ’Ya’yanta 6 A Kano “Da farko…
Shugaban Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari na jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya yi Allah-wadai da kisan matar aure da ’ya’yanta shida a Jihar Kano. An kashe Fatima Abubakar mai shekaru 35, tare da ’ya’yanta a gidansu da ke Dorayi Gidan Kwari a ranar Juma’a. Rikicin Cikin Gida Ne Zai Iya Tura Abba Kabir Yusuf Barin NNPP — Shugaban Jam’iyyar a Kano Sanata Doguwa ya yi wannan bayani ne yayin wani taron “Manema Labari” da aka gudanar a Kano ya bayyana lamarin a matsayin abun tashin hankali, kuma ya ce lamarin ya taɓa zuciyar al’ummar Kano. “Na shiga matuƙar…
Shugaban Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari na jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar ne ka iya zama babban dalilin da zai sa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar. Sanata Doguwa ya yi wannan bayani ne yayin wani taron “Menene Labari” da aka gudanar a Kano, inda ya ce matsalolin cikin gida sun yi matuƙar tsanani, tare da haddasa rarrabuwar kai a tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar. Sarki Sunusi II Ya Bukaci Hukuncin Kisa Kan Masu Kashe Mutanen da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba a…
Mai martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sunusi na II, ya bukaci gwamnatin jihar Kano da ta dauki tsauraran matakai wajen hukunta duk wanda aka samu da hannu a kisan gilla, musamman kan mutanen da ba su aikata wani laifi ba. Sarkin ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai, inda ya yi tsokaci kan kisan gillar da wasu ɓata-gari suka aikata wa Fatima Abubakar da ’ya’yanta shida a yankin Chiranci Dorayi Gidan Kwari da ke karamar hukumar Kumbotso, a karshen makon da ya gabata. Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida…
A wasu sassan Jihar Kano, fargaba na ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma, musamman mata masu zaman gida, sakamakon rahotannin kisan gilla da ake samu a ‘yan kwanakin nan. Mazauna wasu unguwanni sun bayyana cewa lamarin ya sa mutane da dama suka fara sauya salon rayuwarsu, musamman ta fuskar tsaro da kula da muhallinsu. Cututtukan Da Yanayin Sanyi Ke Haifarwa A Najeriya Da Hanyoyin Kare Kai Wata mata da ke zaune a yankin Hotoro, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce tun bayan samun labaran hare-hare, ta ƙara tsaurara matakan tsaro a gidanta. “Yanzu ba ma sake…
Yayin da yanayin sanyi ke bayyana a sassan Najeriya, masana harkokin lafiya na gargadin cewa wannan lokaci na zuwa da matsalolin da suka shafi lafiyar bil’adama, musamman sakamakon busasshiyar iska da ƙura da ke yawo daga hamadar Sahara. Lokacin sanyi, wanda kan fara daga ƙarshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar Maris, na rage zafin jiki ƙwarai — yayin da masana suka ce saukar zafi zuwa kasa da kashi 15% kan iya kawo cikas ga wasu muhimman sassan jiki, ciki har da fata, ido, da tsarin numfashi Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya — Masana A…
