Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‎Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu
Bincike Na Musamman

‎Kisan Gilla: Shawarwari Ga Mata Masu Zaman Gida Don Kare Rayukansu

January 19, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Self Defense Small

A wasu sassan Jihar Kano, fargaba na ci gaba da yaduwa a tsakanin al’umma, musamman mata masu zaman gida, sakamakon rahotannin kisan gilla da ake samu a ‘yan kwanakin nan.

‎Mazauna wasu unguwanni sun bayyana cewa lamarin ya sa mutane da dama suka fara sauya salon rayuwarsu, musamman ta fuskar tsaro da kula da muhallinsu.

‎Cututtukan Da Yanayin Sanyi Ke Haifarwa A Najeriya Da Hanyoyin Kare Kai ‎

‎Wata mata da ke zaune a yankin Hotoro, wadda ta nemi a sakaya sunanta, ta ce tun bayan samun labaran hare-hare, ta ƙara tsaurara matakan tsaro a gidanta.

‎“Yanzu ba ma sake buɗe ƙofa kai-tsaye. Sai mun tabbatar da wanda ke kwankwasa. Ko yaro ne, dole sai an yi bincike,” in ji ta.

Jaridar WDN ta ruwaito cewa irin wannan matakan na iya rage haɗarin fadawa hannun masu aikata laifuka.

‎Daga cikin shawarwarin da suke bayarwa ga mata akwai kulle ƙofofi da tagogi da kyau, guje wa barin abubuwa masu haɗari a fili, da kuma koyon dabarun kare kai..

‎Wani masani kan harkokin tsaro ya bayyana cewa koyon self-defence ba wai don kai farmaki ba ne, illa domin samun damar tsira idan aka samu barazana.

‎“Babban buri shi ne tsira, ba faɗa ba,” in ji shi.

‎Haka kuma, ana kira ga mata da su kasance da hanyar kiran gaggawa a kowane lokaci, ta hanyar barin kati a wayoyinsu ko da na kuɗi kaɗan ne, domin neman taimako idan bukatar hakan ta taso.

‎Wasu mazauna unguwannin sun ce yin ihu idan an fuskanci hatsari na daga cikin hanyoyin da ke jawo hankalin maƙwabta, lamarin da kan hana masu laifi cimma burinsu.

‎Baya ga matakan tsaro na zahiri, mata da dama sun ce sun fi maida hankali kan addu’o’i da ambaton Allah, suna mai cewa hakan na basu kwanciyar hankali da ƙarfin guiwa.

‎Masana sun ce haɗa tsaro na zahiri da na ruhi na daga cikin muhimman matakan da za su iya taimaka wa mata su tsira a wannan yanayi da ake ciki.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

BINCIKE: An samu karin kashi 543% a yaduwar cutar dajin dake kama nono a Najeriya

March 4, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

Ƙalubalen da ke gaban sabon Sufeto Janar na ‘yansandan Nijeriya

February 26, 2026

Dakarun Soji Sun Daƙile Harin Lakurawa Kan Wata Kasuwa a Kebbi

February 24, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.