Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‎Cututtukan Da Yanayin Sanyi Ke Haifarwa A Najeriya Da Hanyoyin Kare Kai ‎
Uncategorized

‎Cututtukan Da Yanayin Sanyi Ke Haifarwa A Najeriya Da Hanyoyin Kare Kai ‎

January 18, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
images

Yayin da yanayin sanyi ke bayyana a sassan Najeriya, masana harkokin lafiya na gargadin cewa wannan lokaci na zuwa da matsalolin da suka shafi lafiyar bil’adama, musamman sakamakon busasshiyar iska da ƙura da ke yawo daga hamadar Sahara.

‎Lokacin sanyi, wanda kan fara daga ƙarshen watan Nuwamba zuwa tsakiyar Maris, na rage zafin jiki ƙwarai — yayin da masana suka ce saukar zafi zuwa kasa da kashi 15% kan iya kawo cikas ga wasu muhimman sassan jiki, ciki har da fata, ido, da tsarin numfashi

‎‎Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Masana ‎

‎A cewar Dr. Rabi Sufi daga Asibitin Koyarwa na Mallam Aminu Kano, yanayin sanyi na da alaƙa da yaduwar cututtuka masu shafar numfashi.

‎“A wannan lokaci mutane kan shaƙi ƙura sosai, wanda ke haifar da tari, mura, ƙan-jiki da kuma kaikayin makogwaro,” in ji ta

‎Ta ce busasshiyar iska na janyo bushewar fata, wadda a wasu lokuta kan kai ga tsagewa. Haka kuma tarin ƙura a iska na haddasa ƙaiƙayi ko kumburin ido da matsalolin hanci saboda su ne hanyoyin da ƙura ke shiga jiki.

‎Likitar ta ce akwai mutanen da ke ɗauke da wasu cututtuka tun farko, amma yanayin sanyi kan kara dagula musu lamarin.

‎“Asthma na daga cikin cututtukan da sanyi kan tsananta, musamman idan mutum ya shaƙi ƙura,” a cewarta.

‎Ta ce yanayin sanyi na janyo raguwa a danshin jiki, wanda hakan kan raunana garkuwar jiki, lamarin da ke haddasa samun matsala ga masu fama da cutar sikila.

‎Masana na ba da shawarar mutane su kula da suturarsu, musamman a lokacin da iska ke da tsananin sanyi.

‎Farfesa Isa Sadiq Abubakar, kwararren likita a AKTH, ya ce “Ya kamata a rufe jiki sosai. Sanya hula, ɗan kwali ko murfi yana taimakawa wajen rage shigar sanyi cikin jiki.”

‎Ya ƙara da cewa takunkumin fuska na taimakawa musamman ga mutanen da ke da cututtukan numfashi, domin rage shakar ƙura.

‎Ya kuma ja hankalin iyaye da su kula da yadda yara ke sa kaya tare da tabbatar da suna cin abinci mai gina jiki domin ƙarfafa lafiyarsu.

‎“Lokacin sanyi ba lokaci ne mai daɗi ba ga kayan jiki. Kariya ce hanya mafi sauƙi da tasiri,” in ji shi.

‎

‎

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Jami’an ’Yan Sanda Sun Dakatar Da Wasan Tashe A Kano

March 1, 2026

Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami

February 21, 2026

Kotu ta tura Abubakar Malami da iyalansa gidan yarin Kuje

December 30, 2025

‎Siyasar Kano: Shin Kwankwaso Ne Zai Tura Gwamna Abba Jam’iyyar APC ko Kuwa Gaban Kansa Yake Son Yi? ‎

December 29, 2025

Sokoto: Gwamna Ahmed Aliyu Ya Gabatar da Kasafin ₦758.7bn na 2026, Ya Ba da Fifiko ga Tattalin Arziki, Lafiya da Tsaro

December 17, 2025

‎DRDI organizes One-Day Training to Raise Public Awareness on Local Government Budgeting

December 2, 2025
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.