Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‎Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Masana ‎
Bincike Na Musamman

‎Sauyin Yanayi Na Canza Yanayin Sanyi A Arewacin Najeriya  ‎ ‎ ‎— Masana ‎

January 18, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
images (1)

‎A wani yanayi da ba a saba gani ba, an shiga watan Janairu na sabuwar shekara, amma har yanzu yanayin sanyi bai tsananta ba a wasu sassan ƙasar, musamman a yankunan arewacin Najeriya.

‎A al’ada, watannin Disamba da Janairu sukan kasance lokacin sanyi mai tsanani, inda ake samun hazo mai kauri a wasu birane da ƙauyuka na Arewa. Sai dai a wannan karo, al’amarin ya sauya, lamarin da ya jawo damuwa da tambayoyi daga ɓangarori daban-daban na al’umma.

‎Yadda dawowar sanyi ya sauya al’amura a Kano

‎Yayin da wasu ke ganin sauyin yanayi ne kawai da ba shi da wata matsala, wasu kuwa na ganin akwai wasu abubuwa na daban da ke faruwa, wanda ke bukatar kulawa ta musamman.

‎Masana dai sun bayyana cewa wannan yanayi na da alaƙa da sauyin yanayi (climate change), wanda suka ce yana da nasaba da ayyukan da ɗan’adam ke aikatawa, kamar sare itatuwa ba tare da shiri ba, gurbata muhalli, da kuma yawaitar hayaki daga masana’antu da ababen hawa.

‎A cewarsu, duk lokacin da aka fara ganin abubuwan da ba a saba gani ba a yanayi, hakan na nuna buƙatar ɗaukar matakai na gaggawa domin rage illa a nan gaba.

‎Da yake tsokaci kan lamarin, Umar Saleh Anka ya ce matsalolin da sauyin yanayi ke haifarwa ba sa gushewa nan take.

‎“Ba za a iya gyara ko sauya illolin sauyin yanayi cikin ɗan gajeren lokaci ba. Abin da za a iya yi shi ne rage tasirinsa a hankali, da kuma ɗaukar matakan kariya,” in ji shi.

‎Anka ya lissafa wasu matakai da ya ce suna da muhimmanci wajen rage illolin sauyin yanayi, ciki har da:

‎

‎Dasa itatuwa

‎Rage sare itatuwa

‎Amfani da dabarun noma na zamani da ba sa gurbata muhalli

‎Amfani da iri mai jure fari

‎Wayar da kan al’umma

‎Samar da dokoki na musamman kan sauyin yanayi

 

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

BINCIKE: An samu karin kashi 543% a yaduwar cutar dajin dake kama nono a Najeriya

March 4, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

Jihohin Najeriya da suka fi yin kasafin kuɗi mai tsoka a 2026

February 20, 2026

Shugaba Tinubu ya naɗa Sarkin Kano Aminu Ado Bayero a matsayin shugaban kwamitin ciyarwar Ramadan na Ƙasa

February 20, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.