Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Rikicin Cikin Gida Ne Zai Iya Tura Abba Kabir Yusuf Barin NNPP — Shugaban Jam’iyyar a Kano
Siyasa

Rikicin Cikin Gida Ne Zai Iya Tura Abba Kabir Yusuf Barin NNPP — Shugaban Jam’iyyar a Kano

January 20, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20260120 WA0025

Shugaban Jam’iyyar NNPP mai kayan marmari na jihar Kano, Sanata Mas’ud El-Jibril Doguwa, ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka addabi jam’iyyar ne ka iya zama babban dalilin da zai sa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya fice daga jam’iyyar.

Sanata Doguwa ya yi wannan bayani ne yayin wani taron “Menene Labari” da aka gudanar a Kano, inda ya ce matsalolin cikin gida sun yi matuƙar tsanani, tare da haddasa rarrabuwar kai a tsakanin shugabanni da mambobin jam’iyyar.

‎Sarki Sunusi II Ya Bukaci Hukuncin Kisa Kan Masu Kashe Mutanen da Ba Su Ji Ba, Ba Su Gani Ba a Kano

A cewarsa, rashin daidaito a tsarin tafiyar da jam’iyyar, rikicin shugabanci da kuma saɓanin ra’ayi tsakanin NNPP da Kwankwasiyya sun jefa jam’iyyar cikin wani yanayi na ruɗani, wanda hakan ke barazana ga makomar ta a Kano da ma ƙasa baki ɗaya.

“Idan ba a gaggauta magance waɗannan matsaloli ba, akwai yiwuwar manyan ’ya’yan jam’iyyar, ciki har da Gwamna Abba Kabir Yusuf, su fara tunanin sauya sheƙa,” in ji Doguwa.

Ya ƙara da cewa gwamnan na fuskantar matsin lamba daga bangarori daban-daban na jam’iyyar, wanda hakan ke iya shafar aikin gwamnati da kuma manufofin da ya sanya gaba tun bayan hawansa mulki.

Sai dai har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, Gwamna Abba Kabir Yusuf bai fito ya tabbatar ko ya musanta yiwuwar barin jam’iyyar NNPP ba.

Masana harkokin siyasa na ganin cewa rikice-rikicen cikin gida na iya zama barazana ga jam’iyyun siyasa, musamman idan ba a shawo kansu cikin hikima da adalci ba, domin hakan na iya haifar da sauya sheƙa da sauyin tsarin siyasa a yankuna.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Mutanen da ake hasashen za su maye gurbin Mataimakin Gwamnan Kano

March 7, 2026

Majalisar Dokokin Kano ta fara yunƙurin tsige mataimakin Gwamna

March 6, 2026

Yadda Jam’iyyar APC Da ADC Ke Sabinta Rigistar Mambobinsu

March 3, 2026

Jam’iyyun Adawa Sun Yi Fatali Da Sabuwar Dokar Zabe Ta 2026 Wacce Shugaba Tinubu Ya Amince Da Ita

February 27, 2026

Shugaba Tinubu ya taya murna ga waɗanda suka lashe zaɓukan Abuja, Kano da Rivers

February 23, 2026

Abin da ya sa na shiga siyasa tsundum – Sheikh Pantami

February 21, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Bincike Na Musamman

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

By WafsymMarch 11, 2026

Sabbin matakan da Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dauka na fara shirin tsige Mataimakin Gwamna,…

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026

KANO: Farashin Kayan Masarufi Ya Yi Tashin Gwauron Zabi Gabanin Shigowar Azumin Ramadan ‎ ‎

February 12, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.