Gwamnatin Tarayya ta ayyana ranakun 25 da 26 ga Disamba, 2025, tare da 1 ga Janairu, 2026, a matsayin hutu domin bikin Kirsimeti, Ranar Boxing Day, da kuma sabuwar shekara. Sanarwar ta fito ne cikin wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar Harkokin Ciki, Dakta Magdalene Ajani, ta fitar a madadin Ministan Harkokin Ciki, Olubunmi Tunji-Ojo, a ranar Litinin. Nazari: Haɗin Kai, Masana’antu da Ra’ayin Jama’a Kan Makomar Kano Ministan ya buƙaci ’yan Nijeriya su yi amfani da lokacin bukukuwan wajen tunani kan ƙauna, zaman lafiya da sadaukarwa, tare da yin addu’o’i domin zaman lafiya, ingantaccen tsaro da ci gaban…
Author: Wafsym
Kiran haɗin kai da Gwamnatin Jihar Kano ke yi a ƙarƙashin One Kano Agenda ya zo ne a yanayi mai matuƙar muhimmanci, yayin da jihar ke fuskantar ƙalubale na tattalin arziki da zamantakewa. Gwamnatin na mai da hankali kan cika alkawuran ta da kuma buɗe sabbin dama ga ci gaba, amma ra’ayoyin jama’a sun bambanta akan yadda za a cimma waɗannan manufofi. Wasu daga cikin kungiyoyin farar hula da masu ruwa da tsaki sun bayyana damuwa sosai kan yadda rashin tsaro, musamman hare-haren ‘yan bindiga, zai iya raunana ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin yankin arewa-west, ciki har da Kano. Wannan…
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Kwamitin Gudanarwar Jami’ar Northwest, dake nan Kano, bisa nada Shugabar Jami’ar (Vice Chancellor) cikakkiya bayan bin sahihin tsari mai tsawo, adalci da gaskiya. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis. Bash M Bash: Lalacewar Masana’antu Na Jefa Tattalin Arzikin Kano Cikin Barazana Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Zartarwa karo na 35, inda Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar (Pro-Chancellor) ya jagoranci mambobin kwamitin da shugabannin jami’ar wajen kai ziyarar girmamawa domin…
Fitaccen ɗan jarida kuma mai sharhi kan al’amuran yau da kullum, Bash M Bash, ya ce durƙushewar harkokin masana’antu a Jihar Kano na daga cikin manyan dalilan da ke janyo koma baya a kasuwanci da tattalin arzikin jihar. A cewarsa, raguwar ayyukan masana’antu ta raunana sana’o’i da kasuwanci, ta kuma rage guraben ayyukan yi da kudaden shiga ga al’umma. Ya ce idan har ana son Kano ta dawo da matsayinta na cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya da ma ƙasar baki ɗaya, dole ne a dauki matakan farfaɗo da masana’antu. Governor Yusuf Receives first female Northwest University VC, Prof. Amina Bayero…
Kano State Governor, Alhaji Abba Kabir Yusuf, has commended the Governing Council of Northwest University, Kano, for appointing a substantive Vice Chancellor after a rigorous and transparent selection process. This was contained in a statement signed by the governor’s spokesperson, Sunusi Bature Dawakin Tofa on Thursday. Sokoto: Gwamna Ahmed Aliyu Ya Gabatar da Kasafin ₦758.7bn na 2026, Ya Ba da Fifiko ga Tattalin Arziki, Lafiya da Tsaro The Governor spoke during the 35th State Executive Council meeting, where the Pro‑Chancellor of the university led members of the Governing Council and the management on a courtesy visit to formally present Prof.…
Gwamnan Jihar Sokoto, Dr. Ahmed Aliyu, ya gabatar da Kasafin Kudin Shekarar 2026 ga Majalisar Dokokin Jihar don yin duba da amincewa. Kasafin, mai taken ‘Kasafin Ci Gaban Tattalin Arziki da Al’umma,’ an tsara shi ne domin habaka ci gaban tattalin arziki da jin dadin jama’a a jihar. Jimillar kasafin kudin naira ₦758.7 biliyan, inda bangaren tattalin arziki ya samu kaso mafi girma na 41%, bangaren zamantakewa kuma 37%. Bangaren tsaro an ware masa ₦45.26 biliyan domin karfafa zaman lafiya da tsaro a fadin jihar. Haɗin Kai ne Mabuɗin Dawo da Martabar Jihar Kano – Gwamnati Bangaren lafiya an ware…
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na aiwatar da kudirin One Kano agenda, yana mai cewa haɗin kai da aiki tare a matsayin al’umma ɗaya su ne mabuɗin dawo da martabar jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa. Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta ba wa shirin cikakken goyon baya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da al’ummar Kano za su ajiye banbance-banbance su haɗa kai domin ceto jihar. DRDI organizes One-Day Training to Raise Public Awareness on Local Government…
The Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) has organized a one-day training program aimed at educating the public and stakeholders on the process of budget preparation and formulation at the local government level. The Executive Director of DRDI, Dr. Muhammad Mustapha Yahaya, stated that the initiative by his organization is designed to raise awareness about how budgets are formulated and to highlight citizens’ rights to participate in local governance and political processes. Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da…
Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi, a kananan hukumomi. Babban Daraktan Ƙungiyar Tabbatar da Dimokuraɗiyya da Zaman Lafiya ta DRDI, Dr. Muhammad Mustapha Yahaya, ya ce ƙungiyar ta kaddamar da shirin wayar da kan al’umma kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi da kuma yancin da aka ba su a harkokin ƙananan hukumomi da siyasa gaba ɗaya. Gwamnonin Arewa sun bukaci a dakatar da ayyukan hako ma’adanai domin shawo kan matsalar tsaro A cewarsa, aikin nasu…
Gwamnonin yankin Arewa tare da sarakunan gargajiya sun ba da shawarar a dakatar da dukkan ayyukan hakar ma’adinai a Arewa na tsawon watanni shida, sakamakon tsananin damuwa kan tabarbarewar tsaro a yankin. An bayyana wannan shawarar ne a cikin sanarwar bayan taron haɗin gwiwa na Gwamnonin Jihohin Arewa da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Arewa, wanda aka gudanar a fadar gwamnatin Sir Kashim Ibrahim da ke Kaduna. DA ƊUMI-ƊUMI: Rundunar Ƴansanda ta hana goyo a babur a Kano A cewar sanarwar, dakatar da ayyukan hakar ma’adinai zai ba da damar tantance alakar da ke tsakanin hakar ma’adinai, matsalolin tsaro, da ta’addanci…
