Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‎Haɗin Kai ne Mabuɗin Dawo da Martabar Jihar Kano – Gwamnati
Babban Labari

‎Haɗin Kai ne Mabuɗin Dawo da Martabar Jihar Kano – Gwamnati

December 17, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20251217 WA0005 1

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa na aiwatar da kudirin One Kano agenda, yana mai cewa haɗin kai da aiki tare a matsayin al’umma ɗaya su ne mabuɗin dawo da martabar jihar da kuma samar da ci gaba mai ɗorewa.

‎Gwamnan, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano, Umar Farouk Ibrahim, ya wakilta, ya ce gwamnatin jihar za ta ba wa shirin cikakken goyon baya, yana mai jaddada cewa lokaci ya yi da al’ummar Kano za su ajiye banbance-banbance su haɗa kai domin ceto jihar.

‎DRDI organizes One-Day Training to Raise Public Awareness on Local Government Budgeting

‎Ya ce shekaru kusan 40 zuwa 50 da suka gabata Kano na daga cikin jihohin da ake koyi da su a fannoni da dama, ciki har da ilimi, kasuwanci, noma, ci gaban matasa, al’adu da kuma ƙarfafa sarakunan gargajiya da ake girmamawa a faɗin ƙasar.

‎A cewarsa, dawo da wannan matsayi na buƙatar haɗin kai tsakanin ‘yan siyasa, al’umma da masu ruwa da tsaki daga kowane ɓangare. Ya ƙara da cewa hakan zai taimaka wajen fuskantar manyan ƙalubale kamar shan miyagun ƙwayoyi, tare da samar da zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki a jihar.

‎Sakataren Gwamnatin ya bayyana cewa gwamnatin NNPP ta cika kusan kashi 85 cikin 100 na alkawurran da ta yi wa al’umma a lokacin yaƙin neman zaɓe, yana mai tabbatar da cewa ana kan kammala sauran kashi 15 cikin 100. Ya kuma bayyana cewa gabanin zaɓukan fidda gwani na shekarar 2026, gwamnatin na shirin sake sabunta alkawurran ci gabanta domin tabbatar da Kano mai wadata.

‎A nasa jawabin, Kwamishinan Yaɗa Labarai, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga jama’a da su rungumi sadaukarwa da jajircewa a aikin sake gina Kano. Ya ce gwamnatin na tallafa wa tsofaffi da ‘yan fansho da suka shafe shekaru suna hidimtawa jihar, tare da bayyana shirin faɗaɗa irin wannan tallafi zuwa ga tsofaffin shugabannin kananan hukumomi da kansiloli da suka yi aiki tsakanin 2014 zuwa 2023.

‎Taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki ya samu halartar ƙungiyoyin matasa, ƙungiyoyin farar hula da sauran jama’a, inda aka tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban Kano da hanyoyin magance matsalolin zamantakewa da tattalin arziki na jihar, a salo na neman mafita mai amfani.

#kano
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

HARIN FARM CENTRE: Kada A Bari Rikicin Siyasa Ya Lalata Tattalin Arzikin Kano — Abbas Ibrahim

April 29, 2026

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

April 25, 2026

Sarki Sunusi ya caccaki gwamnatin tarayya kan cigaba da ciyo bashi duk da janye tallafin mai

April 24, 2026

An tabbatar da naɗin Dr Muttaqha Darma a matsayin sabon ministan gidaje

April 24, 2026

El-Rufa’i ya sake zargin yunƙurin kama shi

April 21, 2026

Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

April 20, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.