Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi, a kananan hukumomi.
Afrika

Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi, a kananan hukumomi.

December 2, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
img 1764682036609

Ƙungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta Kaddamar da horon Kwana daya don wayar da kan al’umma da masu ruwa da tsaki kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi, a kananan hukumomi.

‎Babban Daraktan Ƙungiyar Tabbatar da Dimokuraɗiyya da Zaman Lafiya ta DRDI, Dr. Muhammad Mustapha Yahaya, ya ce ƙungiyar ta kaddamar da shirin wayar da kan al’umma kan yadda ake gabatar da kasafin kuɗi da kuma yancin da aka ba su a harkokin ƙananan hukumomi da siyasa gaba ɗaya.

‎Gwamnonin Arewa sun bukaci a dakatar da ayyukan hako ma’adanai domin shawo kan matsalar tsaro

‎A cewarsa, aikin nasu a yanzu ya fara ne a jihohin Kano da Jigawa, inda suka zaɓi kananan hukumomi uku-uku domin gudanar da bincike da tattaunawa da jama’a kan bukatun su, da yadda za a haɗa su cikin kasafin kuɗin shekara.

‎

‎Dr. Mustapha ya bayyana cewa babban manufar shirin shine bada dama ga al’umma su bayyana bukatunsu tun kafin a kammala kasafin kuɗi, domin a tabbatar da cewa kuɗin da ake kashewa ya amfanar da jama’a.

‎Ya ce“Gaba dayan shirin an tsara shi ne domin wayar da kan al’umma su san yadda ake gabatar da kasafin kuɗi da kuma yancin da aka basu wajen tsoma baki a harkokin ƙananan hukumomi da siyasa gaba ɗaya. Wannan yana taimakawa wajen ganin gwamnati ta saurari bukatun jama’a kafin kasafi ya fita.”

‎Babban Daraktan ya nuna damuwa kan ƙarancin kuɗin da ake warewa bangaren kiwon lafiya da ilimi, wanda zai iya kawo koma-baya a zaman lafiya da ci gaban al’umma.

‎Ya kara da cewa Rashin bibiyar kasafin kuɗi daga al’umma na daga cikin matsalolin da ke kawo gibin fahimta tsakanin gwamnati da jama’a.

‎Rashin shigar da bayanan jama’a cikin kasafin kuɗi na kara matsalar rashin dacewa tsakanin abin da al’umma ke bukata da abin da gwamnati ke aiwatarwa.

‎Jinkirin majalisu wajen sahale kasafin kuɗi na haifar da shiga sabuwar shekara ba tare da kasafi ba, lamarin da ke ƙara yawan cin hanci da tabarbarewar tattalin arziki.

‎Dr. Mustapha ya shawarci gwamnati da majalisun dokoki su ɗauki matakan gaggawa wajen tabbatar da sahale kasafin kuɗi a kan lokaci da aiwatar da kasafin kuɗi yadda ya kamata, tare da sauraron ra’ayoyin al’umma .

‎Ya ce hakan ne kawai zai taimaka wajen tabbatar da dimokuraɗiyya mai inganci, ci gaban ƙananan hukumomi, da zaman lafiya a Najeriya.

‎

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.