Author: Wafsym

Hukumar Yaƙi da Safarar Mutane ta Najeriya (NAPTIP) ta bayyana cewa ta cafke mutum biyar da ake zargi da hannu a safarar mutane tare da kuɓutar da mutum 24 a filin jirgin sama na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja. Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Vincent Adekoye, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, inda ya ce cikin waɗanda aka kama har da wani mutum da ya yi ƙoƙarin safarar ‘yarsa zuwa ƙasar Iraƙi. Jami’in Ɗan Sanda Ya Harbe Kansa Da Bindiga Bisa Kuskure A Kano Wannan samame ya…

Read More

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa za a yada zaman da za gudanar tsakanin majalisar Shura da Sheikh Lawan Triumph kai tsaye a kafafen yada labarai domin tabbatar da gaskiya da kuma kawar da shakku daga zukatan al’umma. Jami’an Ƴan sanda Sun Kama Mai-Gadi Da Ake Zargi da Sace Yaro Ɗan Shekara Biyu ‎ Sakataren majalisar Shura, Shehu Wada Sagagi, ne ya bayyana haka a taron manema labarai. Ya ce za a fara da aikewa da malamin takardar gayyata wadda za ta ƙunshi rana da lokaci da za a sa shi ya bayyana a gaban kwamitin.

Read More

Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da korar dukkan kwamishinoni da sauran manyan jami’an gwamnati da ke cikin gwamnatinsa. Sanarwar, wadda mai magana da yawun gwamnan, Nelson Chukwudi, ya fitar a daren Laraba daga Fatakwal, ta ce korar ta fara aiki nan take, bayan hukuncin Kotun Koli da aka yanke kwanan nan. Yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya A yayin zaman bankwana da ya yi da mambobin majalisar zartarwarsa domin bikin cikar Najeriya shekaru 65 da samun ƴancin kai, Gwamna Fubara ya gode wa dukkan jami’an da suka yi aiki tare da shi a cikin…

Read More

‎Gwamnatin Jihar Kano ta sake tabbatar da aniyarta na gyara da kare gandun daji, yayin da ta kaddamar da sabbin ma’aikata 100 da za su kula da gandun daji 45 a fadin jihar. ‎ ‎Hakan na kun shine ta cikin wata sanarwar da Maryam Abdulqadir Shugabar Sashimi Wayar Da Kai ta Ma’aikatar Muhalli da Kula da Sauyin Yanayi ta jihar ta fitar ga manema labarai. ‎ ‎ Sanarwar ta kara da cewa Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahir Muhammad Hashim, ya ce an dauki ma’aikatan ne daga kauyukan da ke kusa da gandun dajin domin sauƙaƙa musu aiki da…

Read More

‎Wani jami’in ’yan sanda a Jihar Kano, Aminu Ibrahim, ya rasu bayan ya harbi kansa bisa kuskure da bindiga a yayin aiki a unguwar Hotoro. ‎ ‎Lamarin ya faru ne da safiyar Asabar ranar da misalin ƙarfe 5:40, a cikin harabar kamfanin Basnaj Global Resources Limited, Hotoro. ‎‎Rahotanni sun nuna cewa jami’in, wanda yake aiki a ofishin ’yan sanda na Hotoro, ya shiga bayan gida ne lokacin da abin ya faru. ‎ ‎Jami’an Ƴan sanda Sun Kama Mai-Gadi Da Ake Zargi da Sace Yaro Ɗan Shekara Biyu ‎ ‎Wata majiya ta ce, yayin da bindigarsa ƙirar AK-47 ke rataye a…

Read More

‎Rundunar ƴan sanda na jihar Legas ta kama wani mai-gadi, Amos Kini, bisa zargin satar yaro ɗan shekara biyu a unguwar Elemoro. ‎ ‎A sanarwar da kakakin rundunar, SP Abimbola Adebisi, ta fitar a yau Litinin, an ce mahaifiyar yaron ce ta kai rahoto ga ofishin ƴan sanda makon da ya gabata. ‎ ‎Sanarwar ta bayyana cewa lamarin ya faru ne a ranar 21 ga Satumba, 2025, da misalin ƙarfe 11:50 na dare, lokacin da ma’aikacin tsaronta ya gudu da ɗanta da wayarta ba tare da izini ba. ‎ Hawan Jini: Ƙungiyoyi Sun Yi Gargadi Kan Yaduwar Cutar a Nijeriya…

Read More

‎An bayyana yadda talauci ke ingiza mutane sayar da ƙodarsu a Nijeriya, inda sama da ƙoda 651 aka sayar ba bisa ƙa’ida ba tsakanin 2015 zuwa 2020, tare da samun kimanin dala biliyan 41 a kasuwar fataucin gaɓoɓi ta ɓoye, a cewar Farfesa Aliyu Abdu na Jami’ar Bayero Kano. ‎ ‎Ya bayyana cewa wannan haramtacciyar sana’a ta zama wata ƙazamar kasuwanci ta duniya da ke haɗa dillalai marasa izini, likitoci da masu neman fita daga talauci ta hanyar sayar da sassan jikinsu. Hukumar Alhazan Nijeriya ta fitar da farashin kujerar Aikin Hajjin 2026 ‎ Duk da cewa Dokar Kiwon Lafiyar…

Read More

Allurar rigakafin ƙwayar cutar HIV da ake yi sau biyu a shekara, wadda masana suka yaba da ita a matsayin mafi inganci cikin shekaru da dama, ta jawo martani daga ƴan Najeriya bayan rahotanni da suka nuna za ta iya fitowa a kan kuɗi Naira dubu 70,000 ga kowanne mara lafiya a shekara. Maganin, wanda ake kira lenacapavir, yanzu haka ana kasuwancinsa da sunan Yeztugo a Amurka ta hannun kamfanin Gilead Sciences a kan kuɗin da ya kai Dala 28,000 a shekara, kamar yadda jaridar Sunday PUNCH ta gano. Gwamnan Kano Ya Mikawa Majalisa Sunayen Mutane Biyu Don Nada Su…

Read More

‎Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya mika sunayen mutane biyu zuwa majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da su a matsayin kwamishinoni a cikin majalisar zartarwar jiharsa. ‎ ‎Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Lahadi. ‎ ‎Wadanda Aka Tura Sunayen su ne ‎ ‎1. Barista Abdulkarim Kabir Maude (SAN designate) ‎Barista Maude, dan asalin karamar hukumar Minjibir, mai shekaru 40, ana sa ran zai karɓi kambun babban lauya na ƙasa (SAN) gobe Litinin a gaban Kotun Koli. ‎ ‎Ya kammala karatunsa na…

Read More

Hukumar Alhazai ta Nijeriya (NAHCON) ta sanar da kuɗin Aikin Hajji na shekara mai zuwa ta 2026 da aka ƙayyade kan naira miliyan 8.1, miliyan 8.2 da miliyan 8.5. Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne ya sanar da hakan bayan rattaba hannu kan wasu yarjejeniyoyi da kamfanonin da ke tafiyar da hidimomin alhazai a ƙasar Saudiyya. Wata sanarwa daga sashen yaɗa labarai na hukumar ya fitar ta ce: “Bayan tuntubar duka masu ruwa da tsaki, ciki har da shugabannin jihohi da samun amincewar Gwamnatin Tarayya da Shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ya sanar da kuɗin…

Read More