Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » ‎Gwamnan Kano Ya Karɓi bakuncin Shugabar Jami’ar Northwest Farfesa Amina Bayero. Mace Ta Farko a Jami’ar ‎
Babban Labari

‎Gwamnan Kano Ya Karɓi bakuncin Shugabar Jami’ar Northwest Farfesa Amina Bayero. Mace Ta Farko a Jami’ar ‎

December 19, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
1766131489493

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yaba wa Kwamitin Gudanarwar Jami’ar Northwest, dake nan Kano, bisa nada Shugabar Jami’ar (Vice Chancellor) cikakkiya bayan bin sahihin tsari mai tsawo, adalci da gaskiya.

‎Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a ranar Alhamis.

‎Bash M Bash: Lalacewar Masana’antu Na Jefa Tattalin Arzikin Kano Cikin Barazana

‎Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin zaman Majalisar Zartarwa karo na 35, inda Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar (Pro-Chancellor) ya jagoranci mambobin kwamitin da shugabannin jami’ar wajen kai ziyarar girmamawa domin gabatar da Farfesa Amina Salihi Bayero a hukumance a matsayin sabuwar Shugabar Jami’ar.

‎Farfesa Amina Bayero ita ce Shugabar Jami’a mace ta farko a tarihin jami’ar, wadda ta ta faro tun daga tushe kasancewarta daga cikin ma’aikatan koyarwa na farko tun kafuwar jami’ar mallakin jiha.

‎Gwamna Yusuf ya shawarci sabuwar Shugabar Jami’ar da ta gudanar da aikinta da himma da gaskiya, tare da yin aiki tare da dukkan masu ruwa da tsaki domin bunƙasa ingancin ilimi a tsawon wa’adin mulkinta na shekaru biyar.

‎Ya kuma tabbatar wa sabuwar shugabar jami’ar cikakken goyon bayan gwamnatin jiha wajen magance ƙalubalen da jami’ar ke fuskanta.

‎Gwamnan ya sanar da cewa za a biya dukkan bashin alawus-alawus na koyarwa (Earned Academic Allowances – EAA) da ake bin ma’aikatan jami’ar kafin ƙarshen watan Disamba.

‎Haka zalika, ya ba da umarni ga Kwamishinan ma’aikatar Kasa da Tsara Birane da ya tantance dukkan filayen jami’ar tare da soke duk wani fili da aka bada shi ba bisa ka’ida ba a lokacin gwamnatin da ta gabata.

‎Gwamna Yusuf ya nuna godiya bisa ziyarar da aka kai masa, tare da jaddada bukatar da gwamnatin jiha ke da shi na ganin an samu ingantaccen ci gaban ilimi da bunƙasar jami’ar ƙarƙashin sabon shugabanci.

‎Tun da farko, Shugaban Kwamitin Gudanarwar jami’ar, Farfesa Hafiz Abubakar, ya bayyana cewa zaɓen cikakkiyar Shugabar Jami’ar ya ɗauki tsawon watanni goma, kuma Kwamitin Gudanarwar ya amince da sakamakon baki ɗaya.

‎Ya ƙara da cewa nadin Shugabar Jami’a mace ta farko a jami’ar ya samu karɓuwa sosai daga al’umma.

‎A nata jawabin, Farfesa Amina Salihi Bayero ta gode wa Allah bisa wannan dama da aka ba ta, tare da alƙawarin sadaukar da kanta gaba ɗaya wajen aiwatar da amanar da aka ɗora mata.

‎Ta kuma gabatar da tsare-tsare guda 14 da ke da nufin sake farfaɗo da jami’ar domin samun ingantaccen ci gaban ilimi da na gudanarwa.

‎

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sarkin Gaya: Mallakar Katin Zaɓe Shi Ne Ginshiƙin Zaɓen Shugabanni Nagari

July 3, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

Gwamnatin Tarayya Za Ta Rushe Tsarin Karatu Mai Dauke Da JSS Da SS A Makarantun Sikandire A Najeriya

June 30, 2026

Jami’ar Northwest Kano Ta Kori Dalibai 34 Saboda Karya Dokokin Jarabawa ‎

June 30, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.