Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Za A Fara Rajistar Utme Ranar Litinin – JAMB
Labaran Cikin Gida

Za A Fara Rajistar Utme Ranar Litinin – JAMB

January 25, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
jamb exam1 1

Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu ta Ƙasa (JAMB) ta sanar cewa rajistar UTME 2026 za ta fara ne daga Litinin, 26 ga Janairu, zuwa 28 ga Fabrairu, a dukkan cibiyoyin kwamfuta (CBT) da hukumar ta amince da su a fadin Najeriya.

Shugaban JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya bayyana haka ne a Legas yayin taro da Kwamishinonin Ilimi na jihohi. Ya ce sayar da takardar neman rajista (e-PIN) zai fara daga 19 ga Janairu kafin fara rajistar kai tsaye.

‎“Ya Kamata ‘Yan Jaridu Su Riƙa Nuna Tausayi, Hikima Da Mutunta Jinƙan Ɗan Adam wajen ɗauko labarai ‎ ‎ ‎—Comrade Abbas Ibrahim

Farfesa Oloyede ya kara da cewa zaɓin jarabawar gwaji (mock) zai rufe a ranar 16 ga Fabrairu, yayin da sayar da takardun neman Direct Entry (DE) zai fara daga 2 ga Maris har zuwa 25 ga Afrilu.

Shugaban hukumar ya yi gargadi cewa duk cibiyoyin CBT da ba a iya sa ido a kansu daga hedkwatar JAMB ba za su samu biyan kuɗi, kuma rajistarsu na iya soke wa. Haka nan, ɗalibai ba su da bukatar biyan kowanne ƙarin kuɗi ga cibiyoyin CBT; kuɗin rajista da JAMB ta amince da su kaɗai ake biya.

Ya shawarci ɗalibai su yi rajista da wuri domin samun garuruwan da suka fi so, tare da bayyana duk wani tarihi na rajista ko shiga makaranta da suka taɓa yi, domin kaucewa laifukan rashin gaskiya.

Game da shekarun shiga, JAMB ta ce ɗaliban da za su cika shekara 16 zuwa 30 ga Satumba, 2026, su ne suka cancanci UTME, yayin da ‘yan ƙasa da shekarun za su fuskanci tsauraran gwaje-gwaje na musamman kafin a ba su rangwamen shiga.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Gwamna Abba Ya Kaddamar da Kwamitin Yaƙi da Sha Da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi, Ya Sanya Hannu Kan Dokar Daba A Kano

July 22, 2026

“Rikicin Shaidar Zama Ɗan Ƙasa a Jos North Ya Ɗauki Sabon Salo, Sarakunan Gargajiya Sun Nemi Shiga Cikin Shari’a.”

July 11, 2026

Sahihin ‎Labari Ke Tabbatar Da Amincewar Jama’a, Ba Gaggawar Wallafa Ba- Shugaban NUJ

July 1, 2026

NWUK Expels 34 Students Over Examination Malpractice

June 30, 2026

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 2026

NDLEA Ta Kone Tan 12.2 Na Miyagun Ƙwayoyi a Kano, Ta Kama Mutum 

June 29, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Gwamnatin Kano Ta Yi Alƙawarin Ƙara Wa NDLEA Motoci Don Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ‎

June 29, 20267

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.