Wani sabon bincike da hukumar ƙididdiga ta ƙasa NBS, ta fitar ya nuna cewa mata a Najeriya sun fi maza nesa ba kusa ba wajen yin aikin tiƙi da kula da iyali ba tare da biyansu ba.
Rahoton ya ce mata na shafe kusan kashi 21 cikin 100 na ranarsu, wato kusan sa’o’i biyar, suna yin irin waɗannan ayyuka, yayin da maza kuma kashi 4.1 cikin 100 ne kacal, kusan awa daya kenan suka shafewa.
Dalilin Da Ya Sa Na Ajiye Shugabancin NAHCON – Abdullahi Saleh Pakistan
Binciken, shi ne karon farko da aka gudanar da cikakken bincike a matakin kasa don auna yadda ‘yan Najeriya ke raba lokacinsu tsakanin aikin yi da ake biya da aikin gida da kula da iyali, da kuma hutawa.
Rahoton ya nuna cewa akwai babban giɓi tsakanin mata da maza a ɓangaren nauyin ayyukan gida, a birane da karkara baki ɗaya.
A cewar NBS, ‘yan Najeriya masu shekaru 15 zuwa sama suna shafe kimanin kashi 12.5 cikin 100 na ranarsu, kusan awa uku kenan kan aikin gida da kula da iyali ba tare da biya ba.
Sai dai rahoton ya nuna cewa mata ne ke ɗaukar mafi yawan wannan nauyi.
A yankunan karkara, mata na shafe kashi 24.1 cikin 100 na lokacinsu, kusan awa shida kenan yayin da mazan karkara ke shafe kashi 3.7 cikin 100 ne kawai wajen yin aikin tiƙi.
A birane kuwa, mata na shafe kashi 19.8 cikin 100, yayin da maza ke shafe kashi 4.3 cikin 100.
BBC

