Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Caca na Ci Gaba da Shafar Matasan Arewa, Hisbah Ta Yi Gargadi
Bincike Na Musamman

Caca na Ci Gaba da Shafar Matasan Arewa, Hisbah Ta Yi Gargadi

February 5, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
DNN HAUSA
123

Caca na ƙara yaɗuwa a tsakanin matasan Arewacin Nijeriya duk da haramci da gargadin addini, lamarin da ke jefa matasa cikin talauci da matsalolin rayuwa.

‎A da, ana gudanar da caca ne a fili ta hanyar katin wasa, inda galibi matasa da marasa aikin yi ke taruwa. Sai dai a wannan zamani na fasahar intanet, wayoyin hannu sun ba masu caca damar gudanar da harkarsu a ɓoye, ba tare da sanin iyaye ko al’umma ba.

‎Kotun Bauchi ta yanke wa barawon babur hukuncin kisa ta hanyar rataya

‎Masana sun danganta wannan yanayi da tsananin talauci, rashin aikin yi, da yawaitar amfani da wayoyin smartphone.

‎ Rahotanni sun nuna cewa talauci ya kai kashi 77.7 cikin 100 a yankin Arewa maso Yammacin Nijeriya, abin da ke tura wasu matasa neman hanyoyin samun kuɗi cikin sauri, ciki har da caca.

‎Sha’awar kallon wasannin ƙwallon ƙafa, musamman gasar English Premier League, ta zama hanyar da kamfanonin caca ke amfani da ita wajen jawo hankalin matasa. Wasu daga cikinsu na ganin cewa saninsu kan ƙwallon ƙafa zai ba su damar cin riba, duk da cewa galibi sakamakon ya kan zama asara.

‎A jihar Kano, inda dokar Shari’ar Musulunci ta haramta caca tun shekarar 2000, Hukumar Hisbah na ci gaba da kai samame kan shagunan caca.

‎Duk da haka, harkar na ci gaba da bunƙasa ta kafafen intanet, abin da ke sa hukumomi fuskantar ƙalubalen dakile ta gaba ɗaya.

‎Kididdiga ta nuna cewa zuwa ƙarshen shekarar 2025, kasuwancin caca a Nijeriya ya kai kusan dala biliyan 3.63, kwatankwacin sama da naira tiriliyan 5.6. Masana na gargadi cewa caca na ƙara jefa matasa cikin talauci maimakon magance matsalolinsu.

‎Mataimakin Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano, Dr. Mujahideen Aminuddeen, ya ce, “Caca haramun ce a Musulunci kamar yadda shan giya yake haramun. Abin takaici ne yadda wasu matasa suka daina sana’o’i suka dogara kacokan kan caca. Wannan na iya haifar da matsaloli da dama, ciki har da aikata laifuka da shaye-shaye.”

‎Ya ƙara da cewa, “Muna kira ga iyaye da shugabannin al’umma su sa ido sosai kan yadda matasa ke amfani da wayoyin hannu da intanet. Ayyukan wayar da kai da tsauraran matakai daga hukumomi ne kadai zai rage wannan mummunar dabi’a.”

‎

‎Dr. Mujahideen ya kuma jaddada cewa an ƙirƙiro wasu wasannin caca ne da nufin lalata makomar matasa, lamarin da ke jawo su zuwa aikata laifuka ko shaye-shaye.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

El-Rufa’i ya sake zargin yunƙurin kama shi

April 21, 2026

Dole Najeriya ta samu tsaro – Babban hafsan tsaro

April 20, 2026

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.