Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Kwamishinoni 5, da hadiman gwamnatin Kano 10 sun yi murabus tare da yin mubaya’a ga Kwankwaso ‎ ‎
Kano

Kwamishinoni 5, da hadiman gwamnatin Kano 10 sun yi murabus tare da yin mubaya’a ga Kwankwaso ‎ ‎

January 27, 2026
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
Kwankwaso

Rahotanni sun bayyana cewa, zuwa yanzu Kwamishinoni 5 tare da jami’an Gwamnatin Jihar Kano 10, ne su ka ajiye muƙamansu tare da jaddada biyayya da goyon baya ga jagoran Kwankwasiyya, Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso.

‎Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka raba gari tsakanin Kwankwaso, da Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusif.

‎Shalkwatar tsaron Najeriya ta tabbatar da yunƙurin juyin mulki a watan Oktoban bara

‎Kafar yaɗa labarai ta Arewa Updates ta tattaro wannan adadi ne daga abin da ya bayyana zuwa safiyar ranar Talata 27 ga Janairun 2026.

‎Daga cikin kwamishinonin da su ka yi murabus ɗin akwai ɗan Kwankwaso na cikinsa, Kwamishinan Matasa da Wasanni Mustapha Rabi’u Kwankwaso, Kwamishinan Kimiyya da Fasaha Dr. Yusuf Ibrahim Kofarmata, da Kwamishinan Ayyuka na Musamman Nasiru Sule Garo, Kwamishinan Jin Ƙai Adamu Aliyu Kibiya, da Kwamishinan Tsaron cikin gida AVM Ibrahim Umar, mai ritaya.

‎Haka zalika, akwai suma wasu manyan jami’an gwamnati da su ka ajiye muƙamansu, ciki har da Shugaban Hukumar Jin Daɗin Alhazai ta Jihar Kano Laminu Rabi’u Ɗanbaffa, Shugaban Hukumar Gidan Zoo Sadiq Kura Muhammad, Shugaban Hukumar KARMA Alhaji Hassan Danbappa, da SSA GSM Market Sani Shehu Makarya wanda aka fi sani da Igwe China.

‎Sauran sun haɗar da Walidin Kwankwasiyya Mai Taimaka wa Gwamna kan harkokin Masarautu, da Hajiya A’in Jafaru Fagge, Mai Baiwa Gwamna Shawara kan Yaɗa Kyakkyawan Saƙo, da Mujtaba Muhammad Auwal Jami’in Alhazai na Karamar Hukumar Gwale.

‎Sai kuma Hon. Nafiu Umar Dankura SSA Protocol Abuja, da Aminu Sa’idu Meenan Kwankwasiyya, da Shafa’atu Ahmed LondonBe masu riƙe da muƙamin Babban Masu ɗaukar wa Gwamna rahoto a ma’aikatu daban daban a jihar Kano.

‎A cikin bayanan murabus ɗin, jami’an sun bayyana cewa sauye sauyen siyasa da rikicin da ya kunno kai a jihar Kano, ne suka sa suka ɗauki wannan mataki, tare da tabbatar da ci gaba da mara wa tafiyar Kwankwasiyya da jagoranta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso baya.

‎A ranar Litinin 26 ga watan Janairu, 2026, ne dai gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya koma jam’iyyar APC, a hukumance.

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Kano: Fitaccen Ɗan Kasuwar Man Fetur, Audu Manager, Ya Rasu Yana Da Shekaru 68

June 4, 2026

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.