Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani
Labaran Cikin Gida

Takardar Sakandire Ta Isa Bayar Da Damar Rike Mukamin Siyasa — Shehu Sani

October 6, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
shehu sani

‎‎Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa duk wanda ke son tsayawa takara ko samun mukamin siyasa a Najeriya, abin da ake buƙata kawai shi ne takardar shaidar kammala makarantar sakandare.
‎
‎Shehu Sani ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai, inda ya ce tsarin doka a Najeriya bai tilasta sai mutum yana da manyan takardun karatu kafin shiga siyasa ba.
‎
‎NDLEA ta kama tarin ƙwayoyi da ake shirin safararsu zuwa Birtaniya‎
‎A cewarsa, “Doka ta bayyana a fili cewa takardar shaidar sakandare ta isa mutum ya tsaya takara ko ya samu mukamin siyasa. Abin da ake bukata shi ne kwarewa, hangen nesa, da gaskiya wajen mulki — ba sai mutum yana da digiri uku ba.”
‎
‎‎Ya ƙara da cewa a wasu lokuta, masu digiri da dama ba su da ikon gudanar da shugabanci yadda ya kamata, yayin da wasu masu ilimi mai sauƙi ke da nagartar jagoranci da fahimtar matsalolin jama’a.
‎‎
‎Shehu Sani ya yi nuni da cewa abin da ke da muhimmanci shi ne mutum ya kasance mai kishin ƙasa da hangen ci gaba, ba wai takardun karatu kaɗai ba.
‎
‎Maganganunsa sun jawo muhawara a shafukan sada zumunta, inda wasu ke goyon bayansa suna cewa ilimi ba shi ne auna nagartar shugaba ba, yayin da wasu ke cewa Najeriya na bukatar shugabanni masu zurfin ilimi da hangen nesa domin magance matsalolin da ake fuskanta

sakandire shehu sani takara
Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

Rikicin ACF: Lokaci Ya Yi Na Rushe Tsohon Tsari Da Yin Garambawul —Abbas Ibrahim 

May 12, 2026

Za mu mayar da martani kan harin da aka kai wa jirgin ruwanmu – Koriya ta Kudu

May 11, 2026

Dalilin da ya sa na maida akwatin zaɓena Abuja – Pantami

May 11, 2026

Dangote na shirin gina matatar mai a ƙasar Kenya

May 11, 2026

Samar da Aminci, Shi Ne Farko — Dole a Kawar Da Siyasar Dauka Makamai Daga Fagen Siyasar Kano

May 5, 2026

Pantami ya yi watsi da tsarin maslaha bayan kin daukar shi a matsayin dan takarar gwamnan Gombe

May 3, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Kashi 70 na laifukan da ake aikatawa a Kano sanadin shaye-shaye ne – Ƴansanda

By WafsymApril 25, 2026

Wani rahoton ‘yansanda ya bayyana cewa sama da kashi 70 cikin 100 na manyan laifuka…

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

April 2, 2026

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.