Close Menu
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
Facebook X (Twitter) Instagram YouTube WhatsApp TikTok Telegram
WDN HAUSAWDN HAUSA
  • Labaran Duniya
    • Afrika
    • Turai
    • Asia
    • Arab
  • Rahotanni
  • Siyasa
  • Shirye-Shirye
    • Bincike Na Musamman
    • Shirye-Shiryen Radio
    • Shirye-Shiryen Siyasa
  • Wasanni
  • Bidiyo
  • Game da Mu
    • Tuntube Mu
    • Privacy Policy
WDN HAUSAWDN HAUSA
Home » Datti Baba-Ahmed ya ce ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro “bai da amfani”
Afrika

Datti Baba-Ahmed ya ce ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro “bai da amfani”

November 28, 2025
Facebook Twitter WhatsApp Email Telegram LinkedIn
IMG 20251128 WA0013

Tsohon ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, Yusuf Datti Baba-Ahmed, ya soki matakin Shugaba Bola Tinubu na ayyana dokar ta-ɓaci kan tsaro a faɗin ƙasar, yana mai cewa matakin “bai dace ba, kuma ba shi ke magance matsalar tsaro ba.”

A hirar da ya yi da Arise TV, Baba-Ahmed ya ce dokar ta-ɓacin “ta samo asali ne daga rashin fahimtar ainihin matsalar da ake fuskanta,” yana mai kiran matakin “abin ban dariya da ba zai kawo canji ba.”

Yawan Al’umma Na Iya Tsananta Matsalar Tsaro a Nijeriya-Bankin Duniya

Ya kuma soki shawarar gwamnatin tarayya ta dakatar da gina makarantu a yankunan karkara saboda tsaron makarantun, yana cewa wannan mataki “mai haɗari ne kuma babbar kuskure.” A cewarsa, aikin malamai wajen raya ƙasa ya yi daidai da rawar jami’an tsaro, don haka dakatar da gina makarantu “ba mafita ba ce.”

Baba-Ahmed ya yi watsi da shirin gwamnati na ɗaukar ƙarin jami’an tsaro 50,000, inda ya bayyana cewa matsalar ba ƙarancin ma’aikata ba ce, illa yawaitar cin hanci da karkatar da kuɗaɗen tsaro.

Ya ce, “Idan aka dakile cin hanci a ma’aikatar tsaro, ‘yansanda kadai za su iya shawo kan matsalolin ta’addanci da fashi cikin makonni kaɗan.”

Dangane da batun ƙirƙirar masu gadin daji, ya ce babu buƙatar hakan saboda rundunonin tsaro na ƙasa tuni suna da ƙwarewar da ake buƙata idan aka ba su ingantaccen jagoranci. Ya kuma tunatar da irin rawar da sojojin Najeriya suka taka wajen daidaita ƙasashen Afrika tun daga shekarun 1970.

LEADSHIP

Share. Facebook Twitter LinkedIn Telegram Email WhatsApp

Labarai masu alaka

‘Ba zan ba ‘yan Najeriya kunya ba’ – Shugaba Tinubu

April 17, 2026

Wannan ce takarata ta ƙarshe – Atiku

April 15, 2026

Shekaru 12 bayan sace ƴan matan Chibok

April 15, 2026

Tsagin ADC ƙarƙashin David Mark ya kori Nafiu Bala da wasu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

April 15, 2026

Hukumomin yaƙi da cin hanci ba su taɓa gayyata ta ba — Pantami

April 14, 2026

An kama jami’an ƴansanda 6 tare da wasu mutane 3 bisa zargin ƙwace da satar mutane a Edo 

April 14, 2026
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

Babu ɓaraka ko rikici tsakanin Abba da Kwankwaso – Gwamnatin Kano

November 4, 202415

Fagen Wasannin DNN Hausa

October 22, 20248

Dorinar ruwa ta lakume mai gadin gidan gonar Sarkin Yauri na jihar Kebbi.

September 23, 20247

Zamu ba wa fannin lafiya fifiko fiye da komai a karamar hukumar Dala – Alh. Surajo Ibrahim Iman

December 20, 20246
SOCIAL MEDIA
  • Facebook
  • Twitter
  • Instagram
  • YouTube
  • TikTok
  • WhatsApp
  • LinkedIn
  • Telegram
KADA A BAKU LABARI
Afrika

Tsarin Tallafin Magani Na Hukumar KACHMA Na Neman Zama Matsala Ga Marasa Lafiya A Kano

By WafsymApril 2, 2026

A Jihar Kano, ana ci gaba da nuna damuwa kan yadda wasu masu anfani da…

Yunkurin Tsige Mataimakin Gwamnan Kano Da Matsayin Doka

March 11, 2026

RAHOTON MUSAMMAN: Tasiri Da Kalubale Rundunar Kano Neighbourhood Watch — Abin da Rahotanni ke Nuna wa Bayan Fara Aiki

March 9, 2026

Kasuwannin Dabbobi A Kano Na Ƙara Bunƙasa, Amma Amfani da “Sha Ka Fashe” Na Barazana Ga Lafiyar Jama’a ‎ ‎—Rahoto na musamman  ‎

February 27, 2026
© 2026 WDN HAUSA. Developed by: ENGRMKS & CO.
  • Facebook
  • Instagram
  • LinkedIn
  • Telegram
  • Twitter
  • Tiktok
  • Youtube

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.