Yayin da ake shirin gudanar da ranar Dimokaradiyya a kasar nan a gobe Alhamis 12 ga watan Yuni, wasu rukunin mutane sun shirya gudanar da zanga-zanga a jihohi 20 na kasar nan.
Cikin wata sanarwa da suka fitar a yau talata, sun ce za a gudanar da zanga-zangar ne sakamakon wahalar rayuwa da rashin tsaro da kasar nan ke fama da shi tare da tabarbarewar al’amura.
Ko’odinetan tattakin na kasa, Juwon Sanyaolu, yace zasu gudanar da tattakin ne a jihohi 20 na kasar nan.
Wasu daga cikin jihohin da zanga-zangar zata gudana sun hadar da Abuja da Edo da Niger da kuma Yobe sai Bornoi da Oyo da Bauchi da Delta da Adamawa.
Sanyolu yace yayin gudanar da tattakin nasu zasu nunawa shugaban kasar damuwar su kan halin da kasar nan ke ciki, tare da kira a samar da daidaito tare da mutunta Dimokaradiyya.