Kwalejin Ilimi ta Isa Kait dake Karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina zata rika shiya taron bita dan tunawa da Gudunmawar da wazirin katsina Marigayi Isa Kaita ya bayar dan tunatar da matasa muhimancin sadaukar da lokacin su wajen bunkasa rayuwar Al’umma da cigaban Kasa.
Shugaban kwalejin Dakta Ismaila Ado Funtuwa ne ya bayyana hakan yayin taron tunawa da gudunmawar da Marigayi Isa Kaita ya bayar lokacin yana raye karo na farko yau Laraba a kwalejin ta Isa Kaita College of Education dake karamar Hukumar Dutsenma a Jihar Katsina.
Ismaila Ado Funtuwa ya kuma CE gudun mawar da Marigayi Isa Kaita ya Bayan Jihar dama Kasa Baki Daya Abu ne da ban zai musaltu ba musamman fanin Ilimi da bunkasa rayuwar Al’umma.
A nasa jawabin Dan masanin Dutse, Hakimin Kiyawa,Alhaji Adamu Aliyu Kiyawa, wanda ya gabatar da mukala kan rayuwar Tsahon wazirin na Katsina da aka sawa Kwalejin su nan sa Wato Isa Kaita College of Education Dutsanma.bayana wasu cikin halaye da Dabi’un Marigayin yayi da ya kamata Dalibai,Matasan da sauran shugabanin suyi koyi dan Samar da cigaba.
Shehu Isa Kaita Daya ne cikin Yayan Marigayi Isa Kaita,ya godewa kwalejin a madadin sauran Yan uwansa tare da alkawarin bayar da gudunmawa duk lokacin da za’a shirya makamancin taron.
Yayin taron tunawa da Marigayi Isa Kaita an kuma mika kyaututtuka da lambobi na yabo ga wasu cikin dalibai da masu bawa makarantar gudunmawa ta fuskoki da ban-da ban