Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, ya dawo gida Najeriya a yamacin yau Laraba Inda ya sauka a filing jirgin Sama na Malam Aminu Kano Bayan gudanar da Ibadar aikin Hajji shekarar 2025.
Abba Kabir Yusif ya dai shafe mako biyu a Kasa Mai tsarkindanbgudanar da aikin hajin Yayin da ya kasance Amirul Haji na Jihar Kano.
Haka kuma Gwamnan ya samu tarba daga manya jami’an Gwamnatin Kano ,shugabanin kananan hukumomin da masu bashi shawara da sauran magoya baya da suka fito daga sasan Jihar Daban-daban.