Hukumar kiyaye hadura ta kasa zata gudanar da bincike Kan musabbabin faruwar hadarin da yayi sanadiyar mutuwar mutanen ashirin da Biyu a nan Kano wanda suka wakilci jihar a bikin wasanni na Kasa da aka gudanar Ogun.
Shugaban hukumar na Kasa Shehu Muhammad,ne ya bayana hakan lokacin da tawagar hukumar kiyaye haduran suka kawo ziyartar ta’aziya gidan gwamnatin Kano a jiya litinin.
Shugaban hukumar kiyaye haduran ta kasa Wanda mukadashinsa Mai Lura da shiya ta daya dake jihar Kaduna Ahmad Umar,ya wakilta,ya kara da cewar yanzu Haka hukumar ta fara bincike musabbabin yaawan faruwar hatsari a gadar ta Yan kifi dake kan titin Kaduna zuwa Kano.
Ahmad Umar,ya kuma ce zasu hada Kai da gwamnatin Kano da sauran jihohi wajen daukar matakan da suka kamata bayana fitowar sakamakon binciken da suka gudanar da maganace matsalar da ake samun sakamakon yawan haduran.
A nasa Jawabin Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusif, wanda Mataimakinsa Comrade Aminu Abdussalam, ya wakilta ya godewa hukumar tare da alkawarin aiki tare dan kaucewa faruwar irin hakan a nan gaba.
Aminu Abdussalam, ya Kuma kara da cewar yanzu haka wadanda ke kwance a asibiti cikin wanda hadarin ya rutsa da su na samun sauki.
Cikin tawagar hukumar kiyaye haduran sun hadar da shugaban hukumar na jihar Jigawa, Kaduna, Katsina da kuma nan Jihar Kano.