Masana a fanin dokokin Tuki na cigaba da bayana takaicin su kan yawan karya dokar amfani da sigina ta alamar shiga kwana ko danjar dake nuna alamun tsayawa da masu ababen hawa ke kin amfani dasu hakan kuma ke jawo asarar dukiya da rayuka sakamakon haifar da hatsari.
A zantawarmu da wasu dake tafiya a babur mai Kada biyu sun bayana cewa da yawan cikin masu mota ko baburin adaidaita sahu na tsayawa ko shan kwana batare da saka alama ba walau danja birki ko sigina Wanda suka ce hakan na jawo hadura kamar Yadda suka Bayana.
Sai dai wasu cikin masu tuka mota da Adaidaita Sahu sun ce tabbas akwai Wanan matsalar Amma suna baking kokarinsu wajen saka alamar tsayawa ko Shiga kwana lokacin da suke Tuki.
Abdullahi Aliyu Labaran shi ne mai magana da yawun Hukumar Kiyaye hadura ta kasa reshen Jihar Kano ya ce akwai hukunci da doka tayi tanadi kuma sun tabbatar da aikin dokar kan masu karya ta musamman ma masu kin saka alamar tsayawa ko shiga kwana dama kin tsayawa a guraren da danja ke bada hannu.
Labaran ya kuma ce sai Al’umma da sauran masu ababen hawa sun fahimci muhimmancin bin dokokin Tukin za a samu raguwar hadura dake jawo asarar dukiya ko rayukan Al’umma.