Author: Wafsym

Hukumar Kula da ingancin abinci da magani ta kasa NAFDAC ta ce ta kama wasu kayayaki marasa Ingancin a wasu kasuwani da manyan kantinan sayar da kayayaki a nan Kano da kudinsu ya kai fiye da Naira Miliyan Dari Biyar. Shugaban hukumar Mai Lura da jihar Kano, Kasim Idris Ibrahim, ne ya bayana hakan a zantawarsa da manema labarai a yau Jumma’a a shelkwatar hukumar dake sakatariyar Gwamnatin tarayya dake Kan titin zuwa Katsina a nan Kano. Idris Ibrahim, ya Kuma ce yanzu haka sun fara bincike kan mutanen da suka kama da kayayakin dan daukar mataki na gaba. Kasim…

Read More

Shugaban babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam’iyya mai mulkin kasar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa. A hirarsa da BBC Ambasada Damagun ya ce shi kam tsakaninsa da masu zargin cewa shi ɗan-amshin-shata ne na jam’iyyar APC, ba a bin da zai ce sai, ”Allah Ya isa.” Ya ce : ”Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan Kazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a, in da zan shiga jam’iyyar APC…

Read More

Makusantan matashiyar nan da ta yi suna bayan jan hankalin gwamnatin jihar Sokoto kan matsalar tsaro sun tabbatar wa BBC cewa an tsince ta a wani daji na jihar Zamfara bayan batan-dabon da ta yi. Tun ranar Talata ne aka bayar da rahoton ɓatan Hamdiyya Sidi Sharif, bayan ta fita domin zuwa kasuwa, lamarin da ya sanya ta kasa bayyana a zaman kotu kan shari’ar da ake mata a ranar Laraba a Sokoto. A watannin baya ne dai gwamnatin jihar Sokoto ta shigar da matashiyar ƙara a gaban kotu, bisa zargin ta da aikata laifin tunzura tayar da zaune tsaye,…

Read More

Gwamnatin Najeriya ta shigar da ƙarar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, saboda zargin ɓata suna da ta yi a gidan talabijin kai-tsaye. Gwamnatin na zargin dakatacciyar ƴarmajalisar, da ”yin ƙage, duk kuwa da ta san cewa hakan zai shafi ƙimar mutum”, tana mai kafa hujja da cewa yin hakan laifi ne da ke ɗauke da hukunci ƙarƙarshin sashe na 392 na kundin tsarin mulkin ƙasar. Daga cikin jerin mutanen da gwamnatin da sanya a matsayin shaidun da za su tabbatar da zargin, har da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello. Ɗaya…

Read More

Hukumar zaɓen Najeriya, INEC a bayyana aniyarta na fara amfani da fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI wajen gudanar da ayyukan zaɓe a ƙasar. Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar ta hannun babban kwamishinta kuma shugaban kwamitin wayar da kai da yaɗa labarai, Sam Olumekun, ta ce fasahar za ta taimaka wajen sauƙaƙa wa hukumar ɗaukar matakai la’akari da bayanan da za ta samu ta hanyar fasahar. ”Haka kuma fasahar za ta ƙara ƙarfafa sahihancin zaɓuka ta hanyar tattara alƙaluma da kuma tantance aihinin alƙaluman zaɓe”, a cewar sanarwar. Tuni dai hukumar ta sanar da kafa sashen fasahar ƙirƙirarriyar basirar…

Read More

Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya bukaci kafafen yada labarai dake jihar nan dasu rika yin aikinsu cikin gaskiya da rikon amana wajen yada labaran gaskiya Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar shuwagabannin gidan talabijin na Abubakar Rimi karkashin jagorancin Hajiya Hauwa Isah Ibrahim suka kawo masa ziyara a fadar sa. Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu yace kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma. A nata jawabin shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta bayyana cewa sunzo…

Read More

Wata Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin cewa kwacewa da kuma rushe wani gini mallakin wani kamfanin mai zaman kansa baya bisa ka’ida, inda ta umarci gwamnatin jihar Kano ta biya kamfanin diyyar naira miliyan Dubu Biyu da Kuma miliyan Shida. Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad Karaye ya yanke wannan hukuncin, da yayi fatali da matakin da Gwamnatin jihar Kano lokacin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dauka na kwace damar mallakar wuri mallakin kamfanin,ba tare da bayar da wa’adi ba. Kotun ta bayar da umarnin ne,bayan sauraron bangaren masu kara,ta hannun lauyan su Barister Sa’idu Muhammad Tudun wada da…

Read More

Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kashe fiye da Naira Biliyan Biyu wajen karbo shidar kammala karatun Dalibai Tamanin da Hudu Yan asalin jihar da suka Gama jami’ar Near East dake kasar Cyprus a shekarar dubu biyu da ashirin da daya tare da daukarsu aiki. Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusif,ya bayana hakan lokacin da yake mikawa daliban shidar kammala Jami’ar da yammacin jiya Alhamis a dakin taro na Coronation dake gidan Gwamnati. Gwamna Abba Kabir Yusif,ya kara da cewar tuni ya bayar da umarnin daukar daliban aiki Duba da mahimmancin abunda suka koya da kuma bunkasa jihar musamman a…

Read More

Gwamnatin jihar Kano ta ce bazata lamunci Jan kafa ba wajen ajiye mutanen da ake tuhuma da laifi a gidan gyaran Hali tsawon shekaru fiye da biyar zuwa goma batare da yimisu hukumci ba. Gwamnan jihar Abba Kabir Yusif, ne ya bayana hakan yayin Zaman majalisar zartarwa Karo na ashirin da takwas da ya gudana yau litiniin a rukunin gidajen na kwankwasiya dake Unguwar dan Gwauro a nan kano. Gwamnan wanda yayin bayani cikin harshen turanci ya kara da cewar abunda suka gani lokacin da suka ziyarci gidajen gyaran Hali da ke Janguza da Gwauron Dutse sun tarar da mafi…

Read More

Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya yi watsi da rahotanni da ke alaƙanta cewa yana daf da komawa wata jam’iyya, da kuma batun cewa zai shiga haɗaka da wasu jam’iyyu, lamarin da ya ce ƙanzon kurege ne kawai domin ba da yawunsa ba. Dan takarar shugaban ƙasa karashin jam’iyyar NNPP a zaɓen da ya gabata, ya ce raɗe-raɗen ba su da tushi balle makama kuma labaran ƙarya ne kawai na siyasa. “Na daina yin tsokaci kan lamuran siyasa da ke faruwa a Najeriya… kuma zan ci gaba da yin haka har zuwa wani lokaci,” in ji Rabiu Kwankwaso. Don haka ne,…

Read More