Shugaban babbar jam’iyyar hamayya a Najeriya, PDP, Ambasada Umar Iliya Damagun, ya musanta zargin da wasu ke yi masa cewa yana yi wa jam’iyya mai mulkin kasar, APC aiki ne shi ya sa rikicin PDP din ya ki ci ya ki cinyewa.
A hirarsa da BBC Ambasada Damagun ya ce shi kam tsakaninsa da masu zargin cewa shi ɗan-amshin-shata ne na jam’iyyar APC, ba a bin da zai ce sai, ”Allah Ya isa.”
Ya ce : ”Allah ya isa tsakanina da duk wanda ya yi min wannan Kazafi, kuma Allah Zai yi mana shari’a, in da zan shiga jam’iyyar APC da tun lokacin Buhari da na shiga.
”Kuma ina da tarihi tun da na shiga jam’iyyar PDP a 1999 ban taɓa sauya sheka ba. Dole wanda ba ya so na zai nemi yanda zai yaɓa min zargi don ya samu biyan buƙatarsa. An ce ma na je na yi mitin da Tinubu, a Ingila, wannan duk masu yin wannan na bar su da Allah.” In ji shugaban na PDP.