Hukumar Kula da ingancin abinci da magani ta kasa NAFDAC ta ce ta kama wasu kayayaki marasa Ingancin a wasu kasuwani da manyan kantinan sayar da kayayaki a nan Kano da kudinsu ya kai fiye da Naira Miliyan Dari Biyar.
Shugaban hukumar Mai Lura da jihar Kano, Kasim Idris Ibrahim, ne ya bayana hakan a zantawarsa da manema labarai a yau Jumma’a a shelkwatar hukumar dake sakatariyar Gwamnatin tarayya dake Kan titin zuwa Katsina a nan Kano.
Idris Ibrahim, ya Kuma ce yanzu haka sun fara bincike kan mutanen da suka kama da kayayakin dan daukar mataki na gaba.
Kasim Idris Ibrahim,ya kuma ce akwai bukatar masu siyan kayayyaki su tabbatar sun duba lambar hukumar a jikin kayan da zasu siya dama lokacin karewar amfaninsa dan kaucewar ci ko amfani da kayan da zai cutar da su.
Wakilimu Abba Muhammad, ya rawaito cewar hukumar ta kuma sha alwashin cigaba da kakabe duk wasu gurbatatun magani ko kayan abinci da suka saba dokar hukumar.