Gwamnatin jihar Kano ta ce ta kashe fiye da Naira Biliyan Biyu wajen karbo shidar kammala karatun Dalibai Tamanin da Hudu Yan asalin jihar da suka Gama jami’ar Near East dake kasar Cyprus a shekarar dubu biyu da ashirin da daya tare da daukarsu aiki.
Gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusif,ya bayana hakan lokacin da yake mikawa daliban shidar kammala Jami’ar da yammacin jiya Alhamis a dakin taro na Coronation dake gidan Gwamnati.
Gwamna Abba Kabir Yusif,ya kara da cewar tuni ya bayar da umarnin daukar daliban aiki Duba da mahimmancin abunda suka koya da kuma bunkasa jihar musamman a fannin kiwon lafiya.
Wasu cikin daliban da wakilinmu ya zanta da su sun bayana farin cikin su tare da alkawarin bayar da gudunmawa a fannin kiwon lafiyar alummar jihar Kano.
Yayin taron iyayen daliban sun godewa Gwamna Abba Kabir Yusif, tare da bashi lambobin yabo sakamakon Inganta rayuwar yayan nasu wajen karo karatu da daukarsu aiki.