Wata Babbar kotun jihar Kano ta yanke hukuncin cewa kwacewa da kuma rushe wani gini mallakin wani kamfanin mai zaman kansa baya bisa ka’ida, inda ta umarci gwamnatin jihar Kano ta biya kamfanin diyyar naira miliyan Dubu Biyu da Kuma miliyan Shida.
Mai Shari’a Ibrahim Musa Muhammad Karaye ya yanke wannan hukuncin, da yayi fatali da matakin da Gwamnatin jihar Kano lokacin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ta dauka na kwace damar mallakar wuri mallakin kamfanin,ba tare da bayar da wa’adi ba.
Kotun ta bayar da umarnin ne,bayan sauraron bangaren masu kara,ta hannun lauyan su Barister Sa’idu Muhammad Tudun wada da ya shigar da kara a gabanta tun a shekarar 2019 lokacin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Justice Karaye yace kwace wurin wanda Hukumar kula da kasa tayi a wata wasika data rubutawa kamfanin a ranar 3 ga watan satumba na shekarar 2021,ya saba doka da kuma dokokin kasa.
Haka zalika ya bayyana rashin Jin dadin sa bisa karbe wurin ba bisa ka’ida ba dama rushewa a yayin da maganar ke gaban kotu da yace yin hakan yiwa doka karantsaye ne.