Gwamnatin jihar Kano ta ce bazata lamunci Jan kafa ba wajen ajiye mutanen da ake tuhuma da laifi a gidan gyaran Hali tsawon shekaru fiye da biyar zuwa goma batare da yimisu hukumci ba.
Gwamnan jihar Abba Kabir Yusif, ne ya bayana hakan yayin Zaman majalisar zartarwa Karo na ashirin da takwas da ya gudana yau litiniin a rukunin gidajen na kwankwasiya dake Unguwar dan Gwauro a nan kano.
Gwamnan wanda yayin bayani cikin harshen turanci ya kara da cewar abunda suka gani lokacin da suka ziyarci gidajen gyaran Hali da ke Janguza da Gwauron Dutse sun tarar da mafi yawancin wa’anda ke tsare masu jiran sharia ne fiye da masu zaman hukunci.
Abba Kabir Yusif, ya Kuma ce gwamnatin Kano zata hada kai da shugaban alkaliyar jihar Kano dan daukar matakin da ya kamata wajen gudanar da sharia cikin lokaci.
Gwamnan ya Kuma bukaci alummar jihar Kano da su cigaba da saka jihar cikin adduoinsu tare da bawa gwamnati hadin kai yadda ya kamata dan ciyar da Kano gaba.