Mai martaba Sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu ya bukaci kafafen yada labarai dake jihar nan dasu rika yin aikinsu cikin gaskiya da rikon amana wajen yada labaran gaskiya
Sarkin ya bayyana haka ne lokacin da yake karbar shuwagabannin gidan talabijin na Abubakar Rimi karkashin jagorancin Hajiya Hauwa Isah Ibrahim suka kawo masa ziyara a fadar sa.
Khalifa Muhammadu Sunusi na biyu yace kafafen yada labarai na da muhimmiyar rawar takawa wajen tabbatar da hadin kai da fahimtar juna a tsakanin al’umma.
A nata jawabin shugabar gidan talabijin na Abubakar Rimi Hajiya Hauwa Isah Ibrahim ta bayyana cewa sunzo fadar sarkin ne don kyautata Alaka tare da gabatar da kanta ga mai martaba sarkin.
Wakilin mu na masarautar Kano ya rawaito cewa a yayin ziyarar shugaban na tare da rakiyar mataimakin ta Alhaji Idris Musa Abba ,da daraktan sashin labarai da al’amuran yau da kullum Hajiya Husaina Sa’id Bichi da dai sauran manyan ma’aikatan hukumar.